Daga Dawud bn Yazid, daga babansa ya ji Abi
Huraira yana cewa: Manzon Allah (SAW)
yace :"Shin kun san abin da yake yawan shigar
da mutum wuta? Sahabbai suka ce: Allah da
Manzonsa ne suka fi sani, Sai yace: su ne
Al'aura da Baki/ciki..
Kuma abinda yafi yawan
shigarwa Ajannah sune: Tsoron Allah da
kyawawan dabi'u". [Adabul Mufrad hadith 289].
Kenan yana da kyau mu kula da abin da muke
kaiwa bakin mu, mu tabbatar halal muke zuba
ma cikin mu. Sannan mu kare kan mu daga
shiga gonar da ba namu ba, mutum yayi aure
idan yana da halin yi, idan kuma ba yi da halin
yi sai ya bi koyarwar Annabi don ya kare kansa
daga zina. Allah ya aiko Manzonsa ne (SAW)
don ya koyar da mutane kyawawan halaye da
dabi"u. Don haka mu zama masu kiyaye
dukkanin dokokin musuluci.
Allah Ya sanya mu
daga cikin bayinsa masu rabo. Allah ya sada
mu da dukkanin alkhairiai da albarkatun da ladan
da yake cikin wannan Rayuwa.
Source:
Sadeeya Lawal Abubakar