Shugaban Majalisar Malamai na kunginyar Izalatil Bid’ah Wa’ikamatus Sunnah, JIBWIS na kasa, Shaikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ne zai jagorancin mahajjatan jihar Filito a aikin hajjin wannan shekara. Sanarawar haka ta fito ne daga bakin Gwamnan jihar Filato, Barista Simon Bako Lalong a cikin wata takarda da Daraktan yada labarai na Gwamnan, Samuel Emmuel Nanle ya sanya wa hannu a makon da ya gabata.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Gwamna Lalong ya tabbatar wa mahajjatan jihar cewa gwamnatinsa ta yi kyakkyawan shiri don kula da lafiyarsu, daga nan gida Nijeriya zuwa kasar Saudi Arebiya, don su samu kwarin gwiwar yin aikin hajji a cikin nasara.
Daga nan sai gwamnatin jihar ta nemi mahajjatan da suka kammala biyan kudaden aikin hajjinsu, su bayyana a gaban kwamitin tantance Alhazai, karkashin shugabanci Alhaji Danladi Muhammad, wadanda aka fara zama tun ranar Laraba 29 ga watan Yuli da ya gabata 2015.
Title :
Sheikh Jingir Ya Zama Amirul Hajj A Filato
Description : Shugaban Majalisar Malamai na kunginyar Izalatil Bid’ah Wa’ikamatus Sunnah, JIBWIS na kasa, Shaikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ne zai jagora...
Rating :
5