Bayanai daga birnin Benin na jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya na cewa Allah ya yi wa Alhaji Isa Adamu, sarkin Hausawan Benin rasuwa a daren jiya Juma'a.
Alhaji Adamu mai shekaru 80 ya rasu ne a asibitin koyarwa da ke Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja bayan 'yar gajeriyar jiyya.
Kafin rasuwar tasa dai, Alhaji Adamu ya kasance basaraken gargajiya dan arewa da yafi kowanne da dewa a kan sarauta a kudancin Najeriya.
Marigayin dai ya kwashe tsawon shekaru 58 a matsayin sarkin Hausawan jihar Edo.