Assalamu alaikum Malam ya aiyuka Allah ya saka muku da alkairi. Malam wani saqo naci karo dashi nake neman sanin ingancin sa kafin na aiwatar. Jazakallahu khairan.
"Tsarabar Watan Shawwal Nafilar Annabi Muhammadu S.A.W. A Wannan Watan Na Shawwal AkeyinTa
Annabi Muhammadu S.A.W. A Wannan Watan Na Shawwal Yakeyinta.
Nafila Ce, Ba Wata Wahala, Babu Kuma Jan Lokaci, Amma Sai Tarin Falala Da Ganima. Ga Yadda Akeyin Nafilar:-
Nafila Ce Raka'a 8 Sallama 4, Duk Raka'a 2 Za'ayi Sallama.
Annabi Muhammadu S.A.W. Yakeyi A Duk Wannan Wata Na Shawwal Na Kowacce Shekara.
Kowacce Raka'a FATIHA Kafa 1, QULHUWALLAHU Ko Wacce Da BASMALAH Kafa 25. Raka'a 2. Ayi Sallama A Sake Kawo Wasu Raka'a 2, Kowacce Raka'a Raka'a FATIHA 1. QULHUWALLAHU Ko Wacce Da BASMALAH Kafa 25 Haka Za'ayi Raka'a 8. Idan Da Rana Ne. Karatun A 6oye, Idan Kuma Da Dare Ne Karatun A Bayyane.
Amma Wannan Sallar/Nafilar Kunjita A Arha, Annabi Muhammadu S.A.W. Da Zai Yi Bayaninta Sai Da Ya Rantse Har Sau Uku, Rantsuwa Na Farko Da Annabi Muhammadu S.A.W. Yayi Ya Ce: "Na Rantse Da Ubangijin Da Ya Aiko Ni Da Addinin Gaskiya Da Littafin Gaskiya {ALQUR'ANI} Duk Wanda Yayi Wannan Sallar/Nafilar Raka'a 8 Ba Zai Dago Daga Sujadar Karshe Ba, Face Dukkan Zunuban Sa Allah Ya Gafarta Masa, Gaba Daya.
Kuma Idan Mutum Yayi Wannan Sallar/Nafilar Daga Wannan Ranar Har Shekara Ta Zagayo Dan Aljanne Yake Tafiya A Bayan Kasa. Indai Mutum Yayi Wannan Sallar To Dan Aljanna Ne Kawai Babu Wata Magana, Amma Ba Wai Nine Na Fada Ba, Inji Annabi Muhammadu S.A.W. Manzon Allah S.A.W. Ya Ce Ba Wani Magana Ya Ce: Daga Ranar Kawai Dan Aljanna Ne Yake Yawo A Bayan Kasa Kuma Annabi Muhammadu S.A.W. Bai Fada Ba Sai Da Ya Rantse Ya Ce: "Na Rantse Da Girman Ubangijin Da Ya Aiko Ni Da Gaskiya.
Bishara Ga Muminai Gargadi Ga Kafirai. Annabi S.A.W. Sai Da Ya Rantse Sannan Ya Fadi Wannan Maganar. Indai Mutum. Yayi Nafilar Kafin Ya Dago Da Kai A Raka'ar Karshe Duk Zunuban Mutum Anyi Masa Gafara, Kuma Daga Wannan Lokacin Har Mutum Ya Mutu Yana Matsayin {MAGAFURULLAKA} Ne. Shekara 1 Mutum Yana Matsayin {Notice} Ne Ba'a Rubuta Masa Zunubi Za'a Fada Ma Mala'iku. Ai Wannan Rahama Ne A Gare Mu {Mu Ummati Muhammadu Rasulillahi S.A.W.}"
Sannan Ya Sake Rantsuwa Na 2 Ya Ce: "Na Rantse Da Ubangijin Da Ya Aiko Ni Da Addinin Gaskiya Da Littafin Gaskiya Alqur'ani, Duk Wanda Yayi Wannan Sallar/Nafilar Idan Ana Binsa Bashi, Idan ya Roki Allah, Akan Allah Ya Bashi Abinda Zai Biya Bashin, To Allah Zai Buda Masa Ya Biya Bashin Da Ake Binsa Ba Zai Mutu Ana Binsa Bashin Ba. Annabi Muhammadu S.A.W. Ya Kara Da Cewa Wanda Kuma yayi Wannan Sallar/Nafilar Idan Matafiyi Ne To Allah Zai Kai Shi Lafiya Ya Samo Abin Da Yake So Kuma Ya Dawo Lafiya.
Annabi Muhammadu S.A.W. Ya Kara Da Cewa Idan Kuma Mutum Mabukaci Ne Yana So Ya Roki Allah Wata Bukane Tashi, Ko Ta Wanin Sa, Idan Yayi Wannan Sallar/Nafilar Na Rantse Da Girman Ubangiji Bukatar Sa Zata Biya.
Nafila Raka'a 8, FATIHA 1, QULHUWALLAHU Kafa 25 Kowacce Da BASMALAH, Duk Raka'a 2 Ayi Sallama. Idan Wata Bukata Ce Taka Ko Ta WaninKa Sai Mutum Yayi Nafilar Ta Musamman Idan Ya Roki Allah Bukatar Sa Zata Biya. Annabi Muhammadu S.A.W. Ya Ce: Na Rantse Da Girman Allah Bukatar Zata Biya. Annabi S.A.W. Ko Bai Rantse Ba, Idan Da Hankali Mutum Yasan {IJABA} Zata Samu. Amma Aji Tsoron Allah A Roki Alkhairi".
Annabi Muhammadu S.A.W. Ya Ce: "Na Rantse Da Girman Ubangijin Da Ya Aiko Ni Da Addinin Gaskiya Duk Wanda Yayi Wannan Sallar/Nafilar Allah Zai Halicci Mala'iku Adadin Harufan Da Mutum Ya Biya/Karanta FATIHA Da QULHUWALLAHI Da BASLAMAH Na Kowacce Raka'a Adadin Harafi, harafi Na Sallar, Za'a halicci Mala'ik Adadin Harafin Nafilar Da Mutum Yayi Zasu Dinga Dasa Ma Mutum Itatuwa Na Kayan marmari A Gidan Sa Na Aljanna Daga Wannan Ranar Har Zuwa Tashin Alkiyama. Kuma A Wannan Watan Na Shawwal Akeyinta Idan Watan Ya Fita Shikenan Kuma Sai Allah Ya Kaimu Shekara Mai Zuwa Ga Mai Tsawon Kwana, Idan Mutum Yayi Sau Daya Shikenan Ya Sauke Nauyi Ya Wadatar, Idan Kuma Mutum Ya Kara To Karin Darajar Sane A Wajen Allah. Amman Idan Ta Wuce Wannan Watan Kuma Sai Shekara Mai Zuwa Ga Mai Tsawon Rai.
Kamar Mutum Yayi Yau, Gobe Kuma Mutum Yayi Dan Wata Bukata Tasa Wannan Duk Ba Komai. Kamar Sallar Ce Idan Mutum Yayi Ta Farillah To Ya Sauke Nauyi, Idan Ma Yaso Yayi Ta Nafila.
Yana Da Kyau Idan Kaji Wani Abun alkhairi To Mutum Ya Sanar Da Dan Uwan Sa Mumini/Mumina. Domin Mumini baya Cika Mumini Sai Ya Soma Dan Uwansa Abinda Yake Soma Kansa.
Dan Girman Allah, Dan Soyayyar Kowa Ga Annabi Muhammadu S.A.W. Duk Wanda Zai Kwafa Karya Chanja Wani Abu Ya Barshi Kamar Yadda
AMSA
********
Wa alaikis salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Wadanda suka yin rubutun Wannan nafilar Qarya ce suke yiwa Manzon Allah (saww). Domin babu wata ruwaya Sahihiya ko Dha'ifiya wacce tazo da bayanin irin wannan nafilar.
Muna kira ga mutanen da suke Qirkirar wadannan Qarairayin cewa SUJI TSORON ALLAH SU DENA YIWA ANNABINSA QARYA. Domin duk wanda yayi ma Annabi (saww) Qarya to sakamakonsa shine TSINUWAR ALLAH DA MANZONSA. Kuma JAHANNAMA ita ce makomarsa sai dai in ya tuba yayi nadama kafin mutuwarsa.
Allah yana cewa "HAKIKA WADANNAN DA SUKE CHUTAR DA ALLAH DA MANZONSA, ALLAH YA TSINE MUSU ADUNIYA DA LAHIRA. KUMA YA TANADAR MUSU DA WATA IRIN AZABA MAI WULAKANTARWA".
Wannan ya hada da masu Qirkiro masa Qarya ko zagi. Har da masu turowa a internet ko ta Whatsapp ko facebook, etc.
Allah shi kiyayemu. Aaameeen.
WALLAHU A'ALAM.