Assalamu alaikum Malam. Allah ya Qara maka albarka bisa wannan aikin alkhairi da ka assasa mana a facebook. Tambaya nake dauke da ita kamar haka:
Ina cikin yin ramukon azumin da ake bina na Ramadhan, Rannan sai Maigidana ya nemeni da rana alhali ya riga yasan cewa ina azumi. Nace masa babu kyau saduwa da rana idan mutum yana Azumi.. To amma duk da haka bai dena jana da wasa ba.
kuma naga ya matsu sosai sai na biye masa... To shin yanzu sai nayi azumi sittin kenan amadadin wannan? Ko kuma ciyarwa zanyi shikenan?
Don Allah malam a amsa mana da wuri don musan abinda zamuyi. bissalam ka huta lafiya.
(Daga wata Baiwar Allah).
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah wa barakatuh. Lallai abinda kika aikata bakiyi daidai ba. Bai halatta mutum ya karya azuminsa ba, sai dai idan akwai larurar wata jinya wacce ta taso ma mutum.
Amma hukuncinki shine kije kiyi Istighfari ki tuba zuwa ga Allah Madaukakin Sarki bisa ga laifin da kikayi. Amma babu kaffara akanki Sai dai zaki sake daukar wani azumin amaimakon wancan.
Ana yin kaffarar Azumin farillah ne saboda alfarmar watan Ramadhana. Amma idan ramuko kikeyi to babu kaffara akanki idan kika karya. Sai dai laifi ne yin haka.
WALLAHU A'ALAM.