Assalamu alaikum Malam. da fatan kana cikin koshin lafiya. Allah shi gafarta Malam shin ya halatta mutum ya sadu da Matarsa mai tsohon ciki? (Muna magana ne da matata tace wai babu kyau, shine nace sai nayi fatawa awajen Malam naji yadda bayanin yake).
Allah shi bada ikon ansawa.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh. Gaskiya babu wani nassi wanda ya haramta mu'amalar auratayya tsakanin Mutum da matarsa wacce take dauke da juna. Koda yakai wata nawa.
Sai dai idan Saduwar zata iya haifar mata da matsaloli, ko kuma rashin Jin dadi, ko kuma chutarwa gareta ko ga jaririn da take dauke dashi, to mafi alkhairi gareka shine ka kyaleta. ka hakura.
Manzon Allah (saww) yace "BABU CHUTA, BABU CHUTARWA". Don haka ya kamata ka tausaya ma halin da take ciki, kayi hakuri da ita bisa wannan in dai zata samu chutuwa.
WALLAHU A'ALAM.
pls like our page fb.com/1arewa