Rundunar sojin Nijeriya ta ce za ta murkushe kungiyar Boko Haram ko da Shekau a raye ko kuwa a mace.
Rundunar ta bayyana haka ne bayan wani faifan murya da aka fitar aka ce na Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram ne inda ya musanta cewar an maye gurbinsa, kuma ya ce yana nan a raye.
Kakakin rundunar sojin kasa ta Nijeriya, Sani Usman Kukasheka ya bayyanawa BBC cewar “Mu ba mu damu ba ko shugaban kungiyar Boko Haram yana nan a raye ko a mace, mu dai muhimmin abin da mu ka saka a gaba shi ne na tabbatar da cewar mun murkushe kungiyar Boko Haram nan da watanni uku kamar yadda shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya umarce mu”.
A karon farko kuma Jagoran ya ambaci kansa a matsayin Gwamnan daular musulunci na Afrika ta yamma mai mubaya’a ga kungiyar IS.
Ya kuma kalubalanci Shugaban kasar Chadi da kuma Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari kan umarnin da ya bayar na murkushe su cikin watanni uku.
A baya dai an yi ta rade radin cewar Shekau ya mutu.
A makon da ya gabata ma shugaban Chadi Idriss Derby ya ce an maye gurbinsa da sabon shugaban kungiyar.
A makon da ya gabata ne Shugaba Buhari ya umarci dakarun sojin Nijeriya su murkushe kungiyar Boko Haram cikin wantanni uku.