Cigaba ko ci baya? kullum tambayar da nakewa kaina kenan domin a yanzu dai karuwanci yayi karfi mune maza mune mata dollars sun zauna mana motoci gidaje suturu ga ajiyayyu a account. Hakika in kanajin ana manyan yara to mune Big girls. To amma da de da dan kamfe wannan bamu isa mu saba sai da iznin Hajiya Hasina.
Da farko naso nayi mata taurin kai amma ko uffan bata cemin ba kawai sai ta tashi ta dauko kwalbar data ajiyemin kurwa ta jefata a gidan kankara ai take a nan na fadi ina karkarwa tamkar nice a gidan kankarar. Tun ina iya bata hakuri har na sume a wajen. tun daga ranar na shiga taitayina na zama yar sami'ina wa ada'ana.
Sau da dama nakan buya nasha kukana musamman in na tuna yanda na zama rakumi da akala sai yanda aka jani. Nakanji kaman na kashe kaina in na tuna yanda na rika wulakanta mijina akan kwanciyar aure Mu'azzam har kuka yasha yimin. Amma yau nice ko zan mutu in Hajiya Hasina taso sai na bada hadin kai. Sannan a sanda nake da 'yanci ba kowa nake hulda dashi ba amma yanzu kare da doki indai taso to dole na yarda. Babbar matsalar har luwadi sawa take ayi damu.
Ranar da bazan taba mantawa ba shine ranar da Haja Hasina tasa mukayi tsirara ta umarci wasu maza dasu kwanta damu kwanciya iri iri ana dauka a na'ura wai ashe siyarwa tayi ga masu cassette na blue film. WAYYO KAINA inji Halima a da Mamalina a bariki.
Shekararta uku cikin wannan ukuba a lokacin Samira Burger na tsaka da jinyar ciwon sanyi data kwaso a kasar thailand duk ta lalace ta rame. Watarana ta dawo saga asibiti ta biyo ta gidan Mamalina cike da murna tana mai yi mata albishir din samun wani gwarzon malami na addini a cikin garin zariya wadda taji ance yana da lakanin karya sihiri da tsafi a jikin dan'adam. Tace "kinga yanzu Hajiya Hasina tana spain mezai hana kanta dawo muje wajensa koma dace?." . Mamalina ta dago idonta da tayi jazur saboda kuka tace "Ni a yanzu mutuwata ta fiyemin rayuwa Samira domin hakika zuciyata bazata jure wannan jarabawar ba..". Samira ta gyara zama cikin mamaki tace "wani abun ne ya faru kuma?" Mamalina tace "zancena ne dai da Ahmad ko kinsan jiya dana kirashi cewa yayI wai ko da ya rasa mace a duniya bazai iya auren karuwa ba.... ta karashe maganar cikin shishshikar kuka.
Ahmad magidancine dan kimanin shekaru 33 Mutum ne mai natsuwa da son addini. Gashi da kyamar fajirci da fasikai. Haduwarsu da Mamalina ya samo asaline watarana da taje office din da yake aiki wajen ubangidansa kasancewar kowa a ofishin ya shaidi fajircin ubangidan nasa yasa ko tantama baiyi ba da kasancewarta karuwa koda batayi laananniyar shigar da tayi ba. Kallo daya yayi mata ya dauke kansa zuciyarsa cike da tsanarta. Amma cikin ikon Allah ji tayi kaman duk duniya bata taba ganin namiji mai haiba kamarsa ba. Cikin hikima da barikanci ta samu numbersa. wasa wasa ta tsinci kanta cikin wani yanayi da bata taba ko jin labarin irinsa ba. Wato so da kaunar Ahmad domin ji take kamar zata iya rasa rayuwarta in bashi. yayinda shi kuma yake jin daya aureta gara ya zauna gwauro to me ma zaiyi da ragowar bariki shi da ya aje mace kamar sadiya a gida. yarinya mai tarbiya da addini.
Cikin tausayawa kawarta Samira tace "mezai hana muje gurin malamin ko Allah yasa ya taimakamiki har akan wannan matsalar ma" Da wannan kalaman ta jawo hankalin Mamalina harta amince suka rankaya tare gidan sheikh Idris mai tafsiri.
Matar malam mai kirki ta taresu cikin karramawa gamida basu shimfida da ruwa suka zauna kafin malam ya gama bada karatu ya shigo. A cikin hirar tasu ne suka bata labarin abinda ke tafe dasu da abinda suke so ayi musu domin a yanzu basu da buri irin su nutsu su bar harkar nan su yi aure. Matar malam ta jinjina lamarin kana ta kara musu nasiha kan kiyaye rayuwar duniya. Suna cikin hirar ne suka ji gyaran muryar malam alamar zai shigo. Daga kan nan da Mamalina tayi idonta ya fada kan na mahaifinta wanda rayi tsammanin ya dade da rasuwa. Duk da girma da gogewa da 'yar tasa tayi baisa kamanninta ya bace masa ba....
Qra qra qaqa..
Angudu ba'atsiraba..!