Tun asali na tsani Hajiya Hasina yayinda ita
kuma na
kula tana yawan shishigemin da yimin
kyaututtukan
alfarma. saboda haka nake dan bata girma
kuma da
karin cewa kawa ce ita ga mummyna. Gashi
yau na
afka komarta sai yanda tayi dani. Hakika
nayi kudi
irin wanda Hajjo take so nayi. Nayi suna
nayi jama'a
yanzu Hajjo ma gidanta harda masu aiki da
motarta
da direba sai abinda takeso takeyi. To
amma yau
gani a masifar da nasan ita kanta tafi
karfinta.
YANZU INA MAFITA??????
Shigowar Samira ce ta katse mata zancen
zucin da
take. Ta dago a sanyaye ta kalli Samira cikin
murya
mai cike da nadama tace "Samira ashe haka
bariki
take?. Hawayen da samira tayi ta kokarin
boyewa ya
kubce ya ziraro kan kumatunta. sannan
cikin
karyayyiyar murya mai nuna halin
kakanikayi tace
"Hakika nima yau na tabbatar da bariki ba
gidan
zama bace da nasan haka bariki take da ban
bar
gidan mijina ba da na gwammace ace ban
waye ba
da nasan haka abun yake da na hakura da
yanda
Allah yayini. Ta waiwayo cikin hawaye mai
matukar
gudu ta akan fuska tace "Nayiwa Allah
butulci
Mamalina na wulakanta aure yau gashi na
fada
komar bariki.....saurara kiji labarina Koda
Ke Allah ya
fiddaki lafiya kya bawa na baya labari don
daukar
darasi..
Ba sunana Samira ba, ba burger babana ya
sanyamin
ba. sunana Zainab shigowa bariki na canja
suna.
Babana malamine mai tarin ilmin addini
haka
mahaifiyata wadda ake kira Malama Binta.
Gidanmu
makarantace ta koyon karatun addini daga
manya
har yara domin mahaifina kan koyar da
yara da safe
samari da yamma manyan maza da dare.
yayinda
matansa biyu wato mamata da kishiyarta
kan koyar
da matan aure da safe zuwa sha biyu.
Hakika mun taso cikin cikakkiyar tarbiyya
da kun kai
hakan yasa maza masu mutunci ke
tururuwar auren
yan gidanmu. Hakace ta faru gareni
ubangiji yayimin
zabi nagari wato Saminu. Saurayi mai
mutunci da
sanin ta kamata. A bangaren rufin asiri
gwargwado
yana dashi. Domin yana da kanti a kasuwar
rimi inda
yake saida kayan daki. Kin dai ganni
mamalina ba
alfahari ba dole a jefani a sahun farko na
kyawawa
kasancewar nayo uwata wadda ta kasance
buzuwar
nijar. kyau ya zamemin lalura domin kuwa
duk da
kamewa da shigar mutunci da nake sai dai
in ban fita
va amma sai kaga maza na tankani.
Tun bana kulawa har na fara jin alfahari da
kyauna.
Watarana bikin kawata ya tashi na samu
halartar
taron duk da cewar ba dabiarmu daya ba.
Amma
kasancewarta mai kokarin sada zumunci
yasa naji
bazan iya sharemata ba. Da karfe biyar aka
tashi
tafiya party nace ni kam ba inda zani amma
Shafa'atu ta matsamin kan cewa in banje
ba na
wulakantata a idon ango domin nira zaba a
matsayin
babbar kawa ta high table. Ganin ranta zai
baci nayi
waya nacewa Saminu sai dare zai zo ya
daukeni
saboda zan tsaya walima ta mata zalla.
Waje yayi waje taro yayi taro samari da
yanmata
kawai ke tafka tsiyarsu. Takure nake waje
daya don
ban saba da irin wannan ba. kawai sai jin
sallama
nayi a kaina na tada kaina na kalleshi
subhanallah
Allah yayi halitta a wajen nan kyakkyawane
na
nunawa sa'a. "sunana Nabhani zanso
kawance dake
in kin bani dama" ji nayi bazan iya musa
masa ba
kawai sai na gyada kai maana na amince.
MAFARI KENAN.
Hakika shaidan makiyi ne fa dan'adam
domin shi
yayi galaba a kaina har na afka tarkonsa na
dinga
ta'annati da ha'intar aure har ta kai na
farajin cewa
aure fa ba wani abu bane face takura da ci
baya.
Bana karajin tsanar aure sai naga sa'annina
wayanda
basuyi ba suna shanawa hankali kwance. A
duniya ba
abunda nake so irin naganni ina shiga irin
wanda
naso ina abunda naso irin na manyan yara
kaman
yanda naji ana kiran duk wadda ta hadu.
Ni nasan ko giyar wake Saminu yasha bazai
taba
sakina ba kai koda naci nasara ya sakeni to
lallai
zansha wuya a gidanmu gun babana domin
bana
mantawa babbar yayarmu ta taba yaji
amma ko
bahasi baba bai bi ba yamata dukan kawo
wuka ya
korata yace ita kadai zata koma yanda tazo.
Don
haka cikin Dare na bankawa dakin Saminu
wuta ya
kone kurmus na rika ihu ina faduwa jamaa
suna
tausayamin.