Cikin rawar jiki na koma na zauna dabas kukan ma na nemeshi na rasa. Uwani caka ta taso tana lallashina gamida kwadaitamin cewa na daure in ina tsoron macijin na kwanta da bokan a akan alqur'anin sau daya ne kawai kuma ba abinda zai sameni domin itama tayi gashi kuma tana rayuwarta kamar kowa. A firgice na dago kai na kalleta. Nace "karki manta mai qur'anin fa shine yayi micijin kina ganin inna kasa kusantar abindaya halitta saboda kar wani abu ya sameni ......... ke tsaya tun a haifeki nasan waazi nake jinsa. inda kinsan waazi ai da baki shigo bariki ba don haka tunda taurin kai zakiyi kije na barki da bokan. Cikin rawar jiki na durkusa gabanta ina rokon ta taimakamin. Ta juya a hankali cikin tausasa murya tayi magana da bokan. Ansha daga kan ya amince a karshe ya yarje akan cewa zai ciremin mahaifa a maimakon abubuwan daya zana.
Wato zan sadaukar da mahaifata don samun duniya. KAICO
Hakika tsafi gaskiyar maishi domin ni dai abinda na sani shine an umarceni na kwanta na daga rigata bayan nayi sai naga ya dauko wani ruwa ya shafamin akan cikina yayi wani surutun da ban fahimta ba. Daga haka sai kawai naga mahaifa a hannunsa batare da naji ko tsikari ba. haka kuma ko kurjewa cikina baiyiba bare yakai ga tsagewa.
Daga wannan lokacin na zama Mafiya a harkar karuwanci domin ni a karuwan ma ajin farko ce domin har sakatariya bake da ita wadda sai ta nema maka izni kan ka ganni. A gefe daya ga uwata a bariki wato Uwani caka ta dauremin gindi domin sai anyi kamun kafa da ita ake samun kaina.
Na fara sanin Hajiya Hasina ne watarana naje gidan Uwani caka wanda na lakabawa mummy na. ina zaune ana min kunshi ta shigo a hargitse jaka da dankwali a hannu tana huci. jikinta da hannunta duk jini, A firgice mummyna ta tareta tana tambayar meya faru. cikin gadara da jin kai tace "ni da Binta benu ne " "me kikai mata Hasina? ashe baki bar zancen nan ba" ta kalli mummyna cikin fusata tace "ashe ma iyayena zina sukai suka haifeni. Ashe bani ce Hasina Damisa ba, wlh ko wacece tasha gabana sai na tureta duk wadda ta ratso gonata saina zubamata kaya kayar ma tsidau mai dafin ratsa kwakwalwa, ba takamarta kyau ba to yau fuskarta ko kare baya kalla ba". Rasss naji gabana ya bada sauti domin ko baa fassara ba nasan yanyankamata fuska tayi. Binta benu itace babbar yarinyarta kaman yanda nake agun Uwani caka wato nima kenan in nayi taurin kai zan iya fuskantar wannan hukuncin. kai bariki gidan laanannu.,.
Allah ya kare mana imaninmu..
Ameeen..!