Baffa ya kalleni duba na tuhuma da bacin rai. Yayin da ni kuma na
sunkuyar da kaina kasa zuciyata na bugu kaman ta fado. Ina shiga gida
yana shigowa jikina ya dau tsuma ina tsoron hukuncin da zai yankemin don
nasanshi da zafi.
Cikin kaushin murya ya daka min tsawar da sai
da jaririn cikina ya harba. "uban waye na ganki dashi?" cikin in ina da
rawar murya nace "Yayan kawata ne ya ganni a asibiti bana jin dadI shine
ya ragemin hanya. shuru yayi kaman tafsirin bai shigeshi ba kawai sai
naji yace "Halima kiji tsoron Allah kinga hakkin aure......" "aa malam
karkayiwa 'yata baki ba akan hakkinta ba haka kawai in bala'inka na
cinka sai ka sauke akan yata ita ta dorama talaucin?
Hajjo ce ta
katseshi baki ba kumfa don tsabar bala'I. koda yake kareni take amma
inajin ba dadi akan yanda take hantarar mahaifina. Juyawa yayi ya fita
waje ransa na kuna. cikin azarbabi ta tambayeni waye taji ance mota. Ni
kuma ba tare da ko dar ba na zayyane mata zare da abawa.
Aikuwa
abinda na tsammata hakan akayi cikin murnarta ta sa hannu ta karbi kudin
dana diba mata acikin abinda Alhaji Nazifi ya bani. Harda gargadina da
cewa na rikeshi da kyau don ban san inda hanyar arzikina take ba. Wasa
gaske alakata ta fara karfi da Alhaji Nazifi duk da cewa ta waya ta
tsaya.
yayinda gefe daya na fara gajiya da cikin dake jikina
domin na fara fahimtar cewa shima wani gagarumin tarnakin ga hanyar data
budemin. Sannan ga wata tsana dana yiwa mu'azzam mijina dama ya lafiyar
giwa bare tayi hauka. Ai fa tsiya da fitsara kala kala. cikin nada wata
shida kawai na shirya da Alhaji Nazifi ya kaini asibiti aka cireshi
cikin sauki.
sai kawai kiran mu'azzam nayi na shirga masa karya
da cewa nayi bari. Dama likitan na Alhaji Nazifi ne don haka koda
Mu'azzam yazo yanda aka tsaramasa haka ya fada. Wata uku da rabuwa da
cikin nan na gyagije kama bani ba. ga kudi da suka fara zamamin sai na
zama sai abinda na tsarawa rayuwata.
kwata kwata yayana na ajesu
gefe daya bare kuma ubansu. Duk kawaici irin na mu'azzam sai daya kai
karata gun Baffa. Fada duniya Baffa yamin nakiji.
Tun Mu'azzam
najin rade radi a kaina har ya ganewa idonsa kiri kiri harkar da nake.
cikin kuka ya je ya zayyanewa Baffana. Tun da Baffa ya sunkuyar da kai
ko tari bai yi ba har Mu'azzam ya tashi ya tafi. Daga kofar gidan ko
soro Baffa bai shigaba yayi gaba uwa duniya har yau banji labarinsa ba.
Faruwar haka maimakon ta sani nadama sai ma ta karamin 'yanci domin duk
da hakurewa da juriyar halina da Mu'azzam yake duk da cewa yasan me
nake aikatawa.
Amma sai dana kureshi yamin saki daya. Cikin farin
ciki na kira Alhaji Nazifi nayi masa albishir. Bayan iddata duk da
cewar iddar ta ganin ido ce domin abinda aure bai hana ba me saki zai
sa.
Cikin farin ciki na lalubi Alhaji Nazifi da maganar aurenmu
kaman yanda yasha fadamin cewa ina ma Muazzam zai sakenI da shi kuma ba
abinda zai hana ya saki daya daga cikin matansa hudu ya maidani
gurbinta.
Amma ga mamakina amsar da ya bani itace "Banda abinki
Lina ta zaayi mutum ya taka kashi da rana yana kallo"(nima dai abdool
haka nagani..duk sakar yan macen da xata bar gidan mijinta dan wani
namiji nasonta..)sorry 4 u selp maxa basu da tabbas danhak mata akula..!
naku har kullin..