Halima nake 'ya daya tilo agun Maryama wadda akafi kira da Hajjo. Kuma 'ya ta uku agun Malam Idris wanda akafi kira da Malam Datti mu kuma yayansa mukan kirashi da Baffa.
Rayuwar itayena kwatankwacin rayuwar Annabi lud a.s ce da matarsa. Domin kuwa mahaifina ya kasance mutum mai tsantseni da gudun duniya bare abinda ke cikinta ya dauke hankali sa. yayinda Hajjo ta kasance ba mutuncinsa ba hatta nata mutunci ba komai bane i dai zata samu kudi. Ina da yayye biyu maza Hasan da Husaini wanda mahaifiyarsu ta rasu ta barsu yayin haihuwar gambonsu wanda shima ya bita. Ance ita macece mai kyawon hali wannan yasa lokacin data rasu Baffanmu ya rika kuka kaman yaro. jin mutuwar ne yasa ta dau lokaci baiyi aure ba abinda ya tilastawa mahaifinsa nemo masa yar abokinsa Wato Hajjo ba tare da laakari da irin tarbiyyar data samu daga mahaifiyarta ba. Na taso a sangarce ba gyara ba kintsi banda fitsara da rashin kunya ba abinda na iya. saboda fadan da yayyena sukemin akan na gyara kaina ya jawo gagarumin rikicinsu da Hajjo wanda dole tasa suka tattara suka koma gidan kakarsu wadda ta haifi babarsu. Tunda nake ban taba jin zikirin daya wuce "kudi sune mutum ba a bakin Hajjo.
A haka na taso har na zama mutum wato na kai munzalin budurci. Inka ganni kaga Hajjo bazaka ce mun hada jini ba. Domin ita ta kasance irin fararen nan da farin ya kasa ceto fuskarsu daga fallasar da muni ke musu a kallon farko da mutum yayi musu. Yayin da ni kuma na kasance baka mai kyawun nunawa saa. kyawun fulanin asali.
Ganin haka yasa Hajjo ta dau burin duniya ta dora a kaina, duk yayin da taje karbar lefen wata to ranar wuni zatayi rana badadin surutu tana yabon kyauna. sai kaji tana cewa "yo wance ma da bata kama kafarki a kyau ba aka kawomata akwati shida ina gake ai sai sha biyu 'yar nan dozin cif gwal har a 'yatsan kafa". Ina da shekara sha bakwai cif na gama sakandire ba tare da shawara ba Baffana ya badani ga dan abokinsa mai suna Mu'azzam. Duk da cewar banso haka ba amma kasancewar Mu'azzam dan gayu gashi kyakkyawa na nunawa a taro yasa na amince duk da dai sai dana sha doguwar masifa. Amma Hajjo kuwa saboda bacin rai har iskoki ta hau ta sauka abinta ba tare da Baffa ya janye ba.
Zamana da Mu'azzam zamane na jin dadi ga macen data san ciwon kanta domin duk da kasancewarsa karamin maaikaci hakan baisa ya gaza wajen fiddani kunya a tsarana ba. Domin ci da sha da sutura iya gwargwado sai dai a gani a guna. Duk da ina cije masa wani sa'in tare da raina masa inta ciyoni na tsiri gaba dashi kwana da kwanaki hakan baisa ya fasa kyautatamin ba. A haka har nayi haihuwar fari 'yayana yan biyu mata aka sanya musu zahra da zainab. Hakika Mu'azzam ya nuna farin cikinsa da samun yaran nan ya kuma nuna bajinta. Amma komai a kushe yake a gurin babar Hajjo kakata wadda tazo ta zaunamin zaman jego.
Shekarar yaran biyu na samu ciki cikin nada wata biyar na fara zuwa awo. Inda na dage nima asibitin kudi zan rika zuwa domin na gaji da bin layin asibitin gwamnati. Ranar da tarihin rayuwata ya fara gurbata kenan. Domin kuwa bayan naje awon ina dawowa a hanya kasancewata doguwa cikina sam bai bayyana ba. sanye nake da doguwar riga da mayafinta mai ruwan sararin samaniya kasancewar ni'imar ciki fatata tayi luf luf na kara kyau da haske. tafe nake cikin natsuwa ina bin gefen titi. sai jin horn nayi a bayana. A tsorace na waiga don gudun kar a makeni. sai naga glass din motar yana kasa a hankali "lallai kudi shine mutum" na tuna da zikirin na Hajjo. wato mutumin duk da ba kyau ya cija na kuzo ku gani ba amma ni'imar dukiya tasashi yayi shar gwanin shaawa ga kwarjini da haiba.
"sannu 'yanmata" yace dani cikin jan aji da nuna isa irinta masu koshi. kawai sai na tsinci kaina ina masa murmushi. cikin kada ido nace haba malam ka ganni da ciki kace min yan mata. Ya leko tare da kashe ido daya yana leka cikina kaman mai neman wani abu kana yace "waima ji yarinya ke yanzu in aka ce miki ki nuna yanda ake daukar cikima kin sanine bare har kice kina dashi. Nayi 'yar dariya gami da tafa hannu kana nace masa to wallahi wanban itace haihuwa ta biyu da zanyi. ya ja
dogon numfashi gamida tabe baki yace "Any way ina zaki yanzu da ranar
nan". Na fadamasa unguwarmu yace na hau mu tafi. ba musu na shige muka
kama hanya.
Tafe muke yana jana da tadi ni kuwa na saki jiki
dashi ina ta zuba kamar mun saba. sai da muka zo unguwar yace "bari in
saukeki a nan kar mijinki ya ganmu tare ko? Nace ai nan unguwar iyayena
ne amma dai saukeni a man din. Da zamu rabu yace "sai a ban number ko na
rikajin ya baby ya kwaba in ba damuwa. cikin sauri nace "a bakomai"
gami da zaro wayata Nokia rakani bandaki na ciro number dan ban haddace
ba na bashi. ya zaro kudi a gaban motarsa bandir din yan wazobia ya
mikamin yace gashi a rika dan cin hanta kinsan masu ciki sai da kayan
kara jini ko. cikin sauri na amshe ina godiya kana na balle murfin motar
na fita. Ina fita mukayi ido hudu da Baffana ya fito daga masallaci...
Hmm kome xe faru kutara ashiri nagaba..