Yau kwananta hudu a asibiti bata san wanda yake kanta ba sakamakon mummunan ganin da tayi. biyar da rabi agogon ya nuna wanda yayi dai dai da budewar idonta. sai dai cikin saa yau ba kamar kullum ba ta farka ne cikin natsuwa duk da idaniyarta na zubar hawaye amma da dama dama wai kibiya a ido. Domin yafi kwanaki da take farkawa da ihu da firgita. "
Mamalina kin tashi?" cewar matar dake gefen gadon bisa yar doguwar masu jinya. Sai a sannan ta farga da mutum a kusa da ita. cikin karaya ta gyada kanta ba tare data damu data share hawayen dake ambaliya ba. "Hajiya Hasina ina mummy na?" ta tambaya tana shessheka. Cikin gyada kai da nuna jimami tace "sai hakuri mamalina Uwani caka Allah yayi mata rasuwa jiya akai sadakar uku".
shuru tayi kaman bataji me ta fadaba kallo daya zakayi mata ka fahimci ta nutsa a tekun tafakkuri (tunani). . Hakuri zakiyi mamalina ita da ta tafi batai gaggawa ba muma duk jiranta muke...... maganar ta makale a fatar bakinta sakamakon wani kallon razana da yarinyar da ta kira mamalina ta watsa mata, kallon mai dauke da bakaken da sai mai yinsu ne yasan wasalinsu.
"Mutuwa? maana nima zan mutu? a ina? a bariki? cikin wannan kazantacciyar rayuwar? mutuwar wulakanci? kai inaaaa" ta karashe maganar cikin rishin kuka mai dauke da tsantsar nadama. Hajiya Hasina ta kalleta haka sasikai tare da kebe baki cikin izgilanci irin na aminan shaidan tace "au au hehehe Allah na dawo wai dan duniya yaga sabon kabari su mamalina an tuna Allah, ke dan kinga mutuwa sai ki kama wata burburwa ashe da kinga yanda mairo mirrow ta mutu sai ki koma gindin kaaba saboda tuba" ta karashe maganarta cikin sakin wani mugun tsaki. A yau ne likita ya sallami mamalina bayan tabbatar da samuwar lafiyarta. Tun data iso gidan suke fama da ita akan ta kwantar da ha kalinta taci abinci.
Ita kuwa ba abinci ba hatta ruwa dacinsa take ji saboda tashin hankalin da take ciki. wannan shine karo na farko da tayi nadama acikin shekaru goman data shafe tana yawon dandi. Taga mutuwar yan bariki kala kala amma bata taba ko jin labarin mutuwa mafi muni irin na uwani caka ba. shin meya jawo mata irin wannan mutuwa? ta tambayi kanta, BARIKI DA SON ZUCIYA taji wata murya acikin kirjinta ta fada. samun kanta tayi tana mai bada gaskiya ga wannan murya ta hanyar girgida kai ba tare da shiri ba.
A firgice ta waiga sakamakon girgizatan da taji anyi. sanye take da doguwar rigar shadda mai ruwan hoda wadda tasha aiki tun daga wuya zuwa kafa Hajiya Hasina ce. Idonta cike da masifa tace ke mamalina ban fa cika jure sakarci ba. ya zaayi aita lallashinki kina wani bankarewa. kin ganni nan shekarata ashirin da biyar a bariki ina tare da uwani tun ina kwace mata saurayi tana kwacemin har muka zama kamo fara in kamo buzuzu mu raba. kinsan kuwa irin wannan kawancen a bariki ba kowa keyi ba.
Amma ban damu da mutuwarta ba sai ke da ko shekara bakwai bakuyi ba. Cikin sanyin jiki tace Hajiya ni ba mutuwar mummy bace a gabana ni gabadaya hankalina ya koma gida.... "Gida?" ta tare mata numfashi cikin tsawa kana ta dora da wata muguwar shewa kaman tababbiya. cak dariyar ta tsaya kamar wadda aka murdawa na'urar tsayarwa. ta dubeta fuska murtuke tace "ke tsaya kiji na fadamiki nice silar barin uwani caka duniya"..
A raxane ta kalleta cikin kaduwa da mamaki. "Eh ta dora cikin gadara da nuna isa. Yanzu fuskarta ta fara sauyawa izuwa wata kala daban mai nuna tsantsar mugunta da rashin imani. "Kaman yanda na fadamiki uwani caka tare muka shiga bariki da ita, amma tashin farko ta hayemin sakamakon mugayen bokaye da matsafan da suka daure mata gindi a harkarta. Na dade ina fakonta sai na samu saa a gun wani matsafi dake can kogi state mai suna Indakuru. shiya bani magani yace indai nayi matsi dashi sannan na kwanta da danta shi kuma ya kwanta da ita to dagani harshi zamu zamaduniya na damawa damu. Amma ita zata bar duniya. Cikin saa na samu yaronta wanda dama mun dade muna harka dashi a boye batare da saninta ba nagayamishi, Amma ban fadamasa zata mutu ba.
shi kuma ya amince domin ya fadamin kudi yakeso kota halin kaka. Ranar lahadin data gabata ne muka shirya da bokanta wanda ta yarda dashi na biyashi makudan kudi tare da shirya masa abinda zai fadamata. ya kirata yace mata yaga wata kofa ta arziki zata budemata amma makiya sunsa abun a gaba. makarin asirin kuwa shine ta kwanta da danta. A daren ta kirani don shawara nima kuma dama haka nake jira sai na nuna matata bar komai a hannuna.
Dama mun shirya kawai sai na kawomata shi yana tangadin karya kamar yasha kayan maye. A haka ya kwanta da ita wanda tun daga haka ta samu ciwo harta shuda. kinga ai da amincewarta ko?.... ta karashe labarin cikin tambaya..
Assha bariki kenan uwa tahaipi danta abariki sannan kuma shima in yagrma ya kwanta da ita auxu billah allah kare mana imaninmu..!