"Kiyi
min afuwa Mama saboda ziyarar bazata dana kawomiki ba tare da izni ba,
kodayake duk a cikin koyarwarki ne. Saboda kin taba gayamin cewa ZIYARAR
RAMUWAR GAYYA BA'A BUKATAR IZNI ko mamana?". ta karashe maganar cikin
murmushi mai kada hantar maza. kana ta cigaba " Dayake ba isasshen
lokaci garemu ba a gurguje nazo na gaisheki na koma amma kafin na tafi
saboda irin rikon amanar da kikamin nima zan sakamaki da mafi kyawon
aiki mamana, nasan zakiyi tunanin kona samu tabin hankali ne saboda nace
rikon amana Eh mana kin rikeni da gaskiya da amana ko abinda ya faru na
kwalliyar da kikamin a fuska ai bake kika yiba hannunki ne yayi don
haka na yanke shawarar rabaki da abinda zai rika jawo miki masifa yana
rabaki da jama'arki haka kawai Dantsito ware min zara zaran yatsun
mamana na hutasshe ta sayen zoben zinare".
Lallai inkaji ki gudu
sa gudu ne bai zo ba domin duk tsiwa da izgilanci irin na Hajiya Hasina
tana gani suka bankareta tare da toshe mata baki cikin sauki Binta benu
tasa kakkaifar wukarta ta datse mata yan yatsunta guda goma cif. kana ta
sanya suka bare mata bakin Hajiya Hasina ta yanke mata harshe sannan
suka umarci Samira da Mamalina wadda tun bayan kama Hajiya Hasina ta
farka dasu bar gidan kan ta ritsa dasu.
Zaune suke gaban Malam
kabiru wanda ya takarkare yana ta zabga addu'o'I akan kwalbar dake
hannunsa. Bayan yayi kamar saa guda yanayi kawai sai ganin Mamalina
sukayi a kasa tana kakarin amai kan kace kwabo tayi wani yunkuri sai ga
bakin abu mai tada hankali yana fita ta bakinta.
Hakika duniya
makaranta ce domin kuwa Halima ta karantu karatu mai wuya. Don haka
yanzu inkaganta kace daga ka'aba ta fito saboda nutsuwa. Takaicinta daya
mutuwar Samira burger sanadiyyar bugun zuciyar farat daya yayinda aka
shaidamata ta kamu da mummunan ciwon nan wato H.I.V.
Taso su rayu
da Samira rayuwar mutunci kaman yanda sukayi ta bariki a baya tare.
Takaici na biyu mummunar mutuwar da Hajjo mahaifiyarta tayi sakamakon
kisan gillar da yan fashi sukayi mata. Hm kudi kenan inbasu ba hutu
indasu ba kwanciyar hankali.
Zaune yake akan teburin ofishinsa ya
takarkare yana ta latsa madannan kwamfutar yayinda idonsa ke kan allon
kwamfutar mai kama da talabijin. karar ahigowar sakon wayar tasa ne ya
dakatar dashi daga abun dayake kana ya mika hannu ta dauko wayar tasa
gamida da latsa madannin da zai bude masa sakon. " Ahmad fatana ka
kasance kodayaushe cikin koshin lafiya tare da iyalanka bakidaya. Ahmad
inaso na shaida maka cewa in akwai abu mafi soyuwa a gareni bai wuce kai
da auranka ba. In maka ta mahaukaci kaf duniya ban taba ji ko ganin da
namijin da zuciyata ke so ba kamarka. Amma kash saboda rashin kamun kai
irin nawa na jawowa kaina asara da kuncin rayuwa na har abada. tabbas
kuncin rayuwa domin inaji a jikina sonka bazai taba barina ba bare har
na samu sukunin sakada son waninka a raina. Ina maka fatan alheri da
cigaba dafatan nima zaka sani a adduo'inka. Nagode mai kaunarka har
abada Halima.". Ga mamakinsa sai jin hawaye yayu yana gudana a kan
fuskarsa. Wuni guda ya kasa tabuka komai saboda tausayin yarinyar dake
ransa. ya kuma jawo wayar a karo na biyu ya ga tabbas sakon adireshin
data taba aikomasa yana nan. ya tuna randa ta aikomasa da sakon tana mai
fadamasa ta bar abinda take yanzu haka tana gida wajen mahaifinta. in
yanaso ga adireshin ya bincika yaji. A karo na farko yaji yana dokin
sake dora idonsa akan kyakkyawar fuskarta.
Karfe takwas na dare
agogon ya nuna daidai da isarsa kofar gidan ga mamakinsa jama'a dankam a
kofar gidan da alama wani sha'ani akeyi. Saura kiris ya fadi sakamakon
mugun labarin da saurayin ke bashi maganar ta rika yawo a kwakwalwarsa
"Halima daya ce a gidanmu kuma itace yanzu zaa kai gidan mijinta"...
Kuka take tun karfinta har muryarta ta dashe ko baka tambaya ba kasan
kukan ya wuce na amarci ko rabo da gida. A cikin wannan halin taji
wayarta tayi tsuwwa ta dauka don karantawa "Halima kanwata amincin Allah
ya tabbata gareki. kasancewarki karkashin wani a yau bani da ikon furta
miki wata kalma....
Alhamdullilah
Nanne qarshen wannan labari nawa.