Tsaye take a kan Mamalina idonta cike da tsananin bala'I gamida mugunta. Ta kara kara kwalbar jikin wutar ktandir din, Mamalina ta kwalla kara cikin dasasshiyar muryarta da tsananin azaba tasa ko fita batayi. A kalla sun dauki awa uku kenan cikin wannan halin amma har yau ko harafi daya bata ji daga mamalina ba, bare tasa ran zata samu inda zata ga Samira.
Ta nisa ta fesar da hucin takaici gamida ajiye kwalbar a gefe ta kalli Mamalina dake tsakanin rayuwa da mutuwa tace "in jurinki taurin kai nina ninkaki a wannan babin yarinya. haka zanta azabtar dake kaman yanda na azabtar da ire irenki harki wuce inda kika fito. Ita kanta Samirar ba tsira tayi ba. Wallahi kinji na rantse miki ko cikin tsohuwarta ta shige sai na zakulota.....Bare ma ba inda na shiga ina nan tare dake sai dai inaga kece yau zaki koma inda kika fito". Ko bata juya ba tasan mai maganar sai dai maimakon abin ta bata mamaki sai ma ya bata dariya. sai da tayi mai isarta sannan ta gintse kama da dai bata taba murmushi ba.
Cikin takun isa ta karaso sukayi ga da ga da Samira kana ta kuma kecewa da dariya ta kuma gintsewa. Sannan tace "lalle yaro bai san wutaba sai ta konashi. yanzu ke Samira in banda ajali na kiranki har kin isa ki tari karen gidana ma bare ni da kaina?. ". Samira tayi murmushin isa itama kana tace " A da kunnen jaki ke firgita kura amma yanzu ta dago yawar domin ta bayyana cewa fatar banza ce ko qashi babu a ciki. ki sani cewa ko ga fulani ba kowace ranace laraba ba balle kice kullum sa'a na tare dake......Cikinfusata ta dago hannu dan kaiwa Samira duka amma kan ta sauke hannun sai ji tayi wani abu ya rike hannun nata an bankareta ta baya. ko bata gwada ba tasan bazata iya kwace hannunta daga wanda yayi mata rikon ba domin tasan ba karamin kato bane.
Ba karamin jarumi bane zai kalli fuskarta ya kuma kallo a karo na biyu saboda yankan dake jikinta bare kuma kayi arba da kakkaifar wukar dake kyalkyali a hannunta Binta Benu ce. Yarinyar da Hajiya Hasina tayiwa yankan wulakanci a fuska duk a dalilin kin bin umarninta da tayi.
Topah barikin kenan kayi ayima..
Koya abin xata kasance..?