Meya kawoki gidana? me kika zoyi? tashi ki ficemin daga gida kan raina ya baci". Wannan ne abinda ya rika furtawa duk da cewa kalaman na nuna fushi amma abun mamaki cikin sanyin murya yake fada kama mai rada.
Tsugunawa tayi cikin murya mai shakewa irin wadda kuka ya gallaba tace "Baffa kamin aikin gafara wallahi na gane kurena, Hajja ce ta sani duk abinda nayi gashi ta barni cikin wahala. Baffa na shiga masifa na rasa mataimaki.....""Ina Hajjon taki ko bazata iya taimakonki bane?" ya fada cikin nuna kosawa da kukanta. "Naje Baffa tace wai to meye nayi biyayya mana ga uwar dakina..." " ke kuwa ai tafi kowa sanin abinda ya dace dake meyasa bazakibi umarninta ba?" ya fada cikin gatse. "Baffa kasheni fa zatayi ka taimakenI don darajar da Allah yayi Annabinsa........
Cikin fusata malam Datti ya zaro wata igiyar guga ya fara tafkarta dashi yana ihun ta fitar masa daga gida. Ganin abun yayi zafi yasanya matarsa ta zari mayafi ta shiga gidan yayanta wato aminin Malam Datti wanda gidansa ke jikin gidan Malam Datti cikin sa'a ta ganshi a gurguje ta fadamasa abinda ke faruwa.
zaune suke a tsakar gida yayinda Samira da Mamalina ke gefe idanunsu na zubar da hawaye yayinda Malam Kabiru da Malam Datti ke gefe Suma sunyi jugum Iya Dije ce kawai ke karaikainar hada ice don dora abinci. Cikin huci Malam Datti ya katse shurun da cewa "Malam Kabiru kai kasan komai gameda labarina tun daga fitowata daga gida har zuwa sanda Allah ya kawoni garinku matsayin baqo. Ba domin kai ba da ban san ina zan shiga ba. Badan kai ba da yanzu kila ina bakin kasuwa ina bara. Alhalin ina da gidana da sanaata amma na barsu duk akan wannan fitinanniyar yarinyar ita da uwarta. yanzu sai da balai ya sameta zatace ta sanni? wallahi kaji na rantse ko zata mutu bazan taimaka mata ba...." cikin zafin rai Malam Kabiru ya katseshi da cewa "Ba lallai sai ka rantse ba ni zanyi iya yina duk da nasan ni ba kowa bane a gabanku amma zan nemi taimakon Allah" Cikin karaya Malam Datti ya kalli abokinsa yace "Malam kabiru baka gane ba ni wannan yarinyar ba yar goyo bace domin ko ka taimaketa zata baka kunya ne......" naji ta bani din meye naka a ciki? ya fada a hasale gamida umartar su Mamalina dasu biyoshi.
Duk abinda ke faruwa idonta akai ta cikin mudubin tsafin da bokan ya bata. Cikin tafasar zuciya tace " Ni zaa ha'inta? lallai yaran nan basu sanni ba. Amma zan nuna musu ni a bariki mama ce...." ta jawo wayarta cikin bugu daya Mamalina dake gaban Malam Kabiru ta daga cikin kashe murya tace "Babyna ya kike" Duk da bugun da kirjinta keyi sai datayi ta maza ta tattare tsoronta kana tace "Lafiya lau mummyna just missing u". Taja numfashin takaici kana tace "Nima kewarki ke damuna baby amma karki damu ina nan tafe hope everything is moving smoothly, systematically and also majestically" Cikin tsananin tsanarta Mamalina tace "yeah everything is fine mum yaushe zaki dawo?. "karki damu soon just take care of yourself for me ok" "ok mum love u" " love u more" Da haka suka kawo karshen wayar tasu kowa na saka mugun nufi akan dan'uwansa yayinda suke watsawa juna dadadan kalaman kalamai.
A SET OF WHITE TEETH DOES NOT INDICATE A PURE HEART.
Tafe suke a hankali cikin motar suna tattaunawa gamedaagunguna da addu'oin da Malam Kabiru ya basu bayan yayiwa Mamalina alkawarin daidaitata da Mahaifinta. kuuuu taja wani mahaukacin birkin daya firgita Samira dake gefe a zaton wani ta kade amma ga mamakinta sai taga ta balle mota da gudu ta fita.
Koda bata taba sashi a idonta ba ta gane cewa shine Ahmad saboda hango kawarta da tayi tsugune gabansa tana kuka. Kanta karasa sai gani tayi yasa hannunsa ya kwarfe Mamalina da mari harta kifa kasa kana ya sa kansa ya wuce ko juyowa baiyi ba balleyaga a wane hali ya barta.
Yau kwananta shida a asibiti batasan ina kanta yake ba sakamakon hawan da jininta yayi fiye da haddi tun ranar da Ahmad ya mareta. kuma a yammacin ne Hajiya Hasina ta sauka kasa Nigeria cike da mugun kudirinta na gyarawa yaran biyu zama wato Mamalina da Samira Burger. Ko me xe faru se mun qara