Kwance take bisa makeken Gadonta mai amfani da na'ura (remote) na kamfanin nan na dubai mai suna Canopy. kallo daya zaka mata ka gane cewa takai kasar sin (china) a barcinta saboda rashe rashe da tayi bata ko motsi.
kararrawar gidan ta dauki rurin dake sanar da mamallakiyar gidan cewa akwai bako a waje. A karo na uku ne ta yunkura da kyar tana tsaki don jin haushin katse mata daddan baccinta da akayi. kai tsaye ta nufi dan makalallen abun mai kama da tarho wanda ke nuna taswirar bakon dake waje.
Tsaye ta hangota idonta fal da hawaye wanda ke nuni da tashin hankali game da ita. kawarta ce samira wanda suka fi kira burger.
Cikin sauri ta shirya a gurguje tabi samira zuwa gidan Hajiya Uwani caka.
Uwani caka itace uwargida gareta wadda tayi mata hanyar zama duk abinda ta zama. Don haka dole hankalinta ya tashi yayinda wani abu ya shafeta. cikin minti goma sha biyar suka iso gidan. Tsananin rudewa da gaggawa yasa ta manta ko kofar motar bata rufeba sai samira ce ta rufe mata.
Cike falon mata ne dankam kaman yanda aka saba sai dai banbacin yau babu yan daudu kamar kullum kuma maimakon shewa da shegantaka yau kowa jikinta lakwas yake fuskoki na nuna jimami.
Bakinta na rawa tace ina Mummy na? kaman hadin baki su duka suka nuna mata kofar dakin karar da ta fito daga dakin ce ta sanyata ba tare da jiran komai ba ta afka. Allah ya raba idanunmu da mugun gani Hajiya uwani caka ce kwance a kan gadon mata biyu na danneta tana zambarwa tana fizgewa yayinda take sa hannayenta biyu tana yago naman Gabanta tamkar tana yagar biredi. cikin karaji take fadar lalatar data shirya a rayuwa tana ihu kamar tababbiya.
Kasa daukarta gangar jikinta tayi wanda hakan ya tilasta mata zama dabas a kasa hawaye na sintiri a fuskarta. Tsawon mintuna kaman ashirin likitan ya karaso don a cewarsu tafiya da ita asibiti tonon asiri ne gareta a wannan hali. bayan yayi mata allura ta samu bacci sai ya koma inda taji ciwo ya takarkare yana mata gyara. Kaman wanda aka hankada haka aka ga likitan ya baje a kasa yana karkarwa wanda hakan yaja hankalinta ita da sauran mata biyun dake dakin don gano abinda ya firgita gabjejen likitan.
yarrr kowaccensu taji a jikinta yayinda suka hango kansa bakikkirin yana kokarin fitowa ta Gaban Hajiya Uwani caka bakinsa shar da jinin da alama yayi watanda dashi MICIJI NE... Yake gangarowa....
Ko ya abinyake kutara ashiri nagaba..