Hajiya Hasina tayi jim na jiran amsa daga Mamalina shurun da taji ne ya tabbatar mata da hudubarta na shiga. Don haka ta samu kwarin gwuiwar dorawa. " Ina so ki gane shi alhaki kwuikuyone ubangidansa yake bi.
Uwani caka ta shuka iskanci da mugunta a rayuwar aurenta domin dan nata ma bana mijinta bane, bokanta ne yayi mata cikin ta kawowa mijin ya karba. Da kanta take fadamin ta haukata kishiyoyinta uku ta kuma haramtawa mijinta jin dadin kowace mace sai ita.
Ita fa tacemin saboda tsabar asiri sai taje wani kauye wanda sai an bi jirgin ruwa sannan a je. wai malamin yayi mata rubutu a al'aurarta sannan ya goge da tasa al'aurar (wal iyazubillah 'yan uwa wannan fa yana faruwa a gaske). Itace fa taje tayi dawafi a ka'aba da janaba a jikinta duk domin duniya to a ganinki duk abinda ya sameta laifina ne?" . A yanzu Mamalina ta shiga wata duniyar da ita kanta bazata iya sanin sunanta ba. A da tunaninta shine takai kwal a sanin bariki sai yanzu ta gane ita jaririyace a harkar.
Maganar Hajiya Hasina ta dawo da ita hankalinta. "ki sani bariki duniyace guda yanda kika shigeta haka zaki taddata. Karki ji ina fadamiki wannan kiyi zaton ni wawiyace na zauna na sanar dake sirrina kaf sannan ki mike ki karkade zani kiyi gaba kiji dadin kararwa, aa yarinya ban fito ba sai dana shirya ki sani daga yau rayuwarki na hannuna... Mamalina ta dago kai a firgice ta kalli Hajiya Hasina kallo mai alamar tambaya. "Eh haka nake nufi domin boka ya fadamin a tare dake arzikina yake kuma na yarda ke kashin arziki ce domin zuwanki ba karamin haukata arzikin Uwani yayi ba.
Don haka a yanzu kurwarki na hannuna in kema kinaso kiyi irin mutuwar uwar dakinki ko mafi muni daga haka to ga fili ga mai doki. Amma kafin na tafi kalli nan" kaman a majigi haka Mamalina taga kwalba irin ta giya ta bayyana a hannun Hajiya Hasina a cikin kwalbar wata halittace wadda babu maraba da ita da take zaune.
Takai awa guda bayan fitar Hajiya Hasina batasan me take tunanowa ba saboda tsabar cunkushewa da kwakwalwarta tayi. "Halima kiji tsoron yaudarar duniya kinga hudubar da uwarki take miki kike ganin dai daine wallahi ba abinda zai ja miki sai nadama a lokacin da nadama bata da amfani, ina jiye miki lokacin da duniya duk girmanta zata zame miki kamar kabarin arne saboda takura. Ina jiye miki lokacin da ga jami'an tsaro kewaye dake suna bawa gangar jikinki tsaro amma ruhinki na dar dar na tsoro da fargaba. A lokacin da zaki ganki cikin dogon gini da kakkarfar kofa amma ki rika jinki kaman a dokar daji kike saboda rashin kariya..." A daidai sanda tazo nan a tunanin kalaman mahaifinta ne sai kuka ya kecemata. "kaico ni Halima bariki batamin gata ba. Hakika innata ta kaini ta baro koda yake nima da son zuciyata. ina kake Babana kazo kaga yanda na zama zokaga kalaman da kake fadamin gasu nan daya bayan daya ina gani, Dana zauna a gidan mijina daka zabamin cikin rufin asiri da yan yarana da ban shiga wannan mummunar rayuwa ba. kowa yaki sharar masallaci yayi coci ma ba kasuwa ba. Yau nakijin nasihar mahaifina mai cike da lallashi. nazo wata banza yar bariki na juyani da karfi".
Cikin wannan halin tunanin rayuwarta ta baya ta dawo mata. Hakika ta yarda alhakin aure masifa ne. Kin jin maganar iyaye bala'ine. Hakika jin dadin duniya ba komai bane. Rayuwar ya mace darajarta shine gidan aure.....ko yaya Mamalina ta bankado kofar shiga bariki?..
like our Facebook page for more Update
1arewa