Motar haya ce ta kwaso fasinjoji daga tashar
unguwa uku da ke Kano zuwa Kaduna. Tun shigowar matashi Nasimat ya yi tozali da
zankadediyar budurwar da ke kusa da shi, hankalinsa ya gushe, ya kamu da
matukar kaunarta. Sai dai fahintar da ya yi mata ta fito daga gidan daula,
saboda suturun da ke jikinsa, za ta yiwu matsalar karfe ce ta sa ta zuwa Kaduna
a motar haya, ko dai wani sanadin. Katuwar waya ce Nokia N9 tana ta
latse-latse. Ya yi tunanin hanyar da zai jawo hankalinta gare shi ya rasa.
Can dubara ta fado masa, in dai 'yar masu hannu
da shuni ce ita ba za ta rasa sanin manyan mutane da sunansu ya watsu a duniya
ba, don haka ya zabi wannan damar, inda ya saka wayarsa a silent sannan ya kara
a kunne. Cikin daga murya yadda duk wanda ke cikin motar zai iya jinsa ya soma
cewa.
"Haba Dangote, ya za ka yi min haka? Ka san
fa mutanen nan an musu alkawarin kujerun makka ga shi lokaci na tafiya har
yanzu ba ka kara magana a kansu ba..."
Ya dan saurara kamar yana jin amsa ne daga Dangoten,
sannan ya dora da fadin.
"Ka rabu da Aminu Dogo, kowa tasa ta fisshe
shi... Ka ga jiya mun hadu da Dahiru Mangal a Dubai ya ce shi ma zai biya wa
mutane dari hajjin bana... A'a, ai ni na fada maka saura mutum daya zan
biyamawa, sauran dari da cas'in da tara duk suna screening... To ya dai kamata
ka san alheri ba shi da kadan... Ni ma ina motar haya don na ga yadda talakawa
ke shan wahala yayin gudanar da zirga-zirgarsu... Eh ai idan dai sun ba mu
hadin kai kowane dan Najeriya sai ya mallaki jirgin kansa... To sai mun yi
waya".
Ya kashe wayar tare da kai dubansa gefensa,
wayyo Allah ai daskarewa budurwar ta yi tana dalalar da yawun da ba ta san
lokacin da ya ke zuba ba. Ba ma ita kadai ba, kafatanin mutanen da ke cikin
motar sun dawo da hankalinsu ga Nasimat illa direban da shi ma ya ke dan
waiwayowa saboda tsaro.