Nasimat ya basar da
irin kallon kurillar da a ke masa, ko banza ya watsa barkonon tsohuwa hanci ya
fara yoyo. Babu dai wanda ya tanka masa, sai dai kadan-kadan budurwar mai amsa
sunan Siyama na satar kallonsa ta dambareren gilashin da ya cike gurbin
fuskarta.
Can da ya ga ba wanda ya kula shi, kuma wadda
aka yi dominta ba ta magantu ba, sai ya saita alamar na mintina biyar. Ya maida
wayar aljuhu, lokaci na cika alarm din ya kada, ya dan basar kafin daga bisani
ya ciro wayar daga aljihu, ya kara a kunne.
"Wai Isah Yuguda ya ka ke so na yi? Na ce
muku bana ba sa'a dole ne na bar jam'iyyar PDP tun kafin ta bare da ni... Duk
wata hidima dai na yi don Allah ku kyale ni".
Ya ja tsaki ya sauke wayar alamar jin haushi.
Siyama ta kasa jurewa, cikin hikima ta dan saki
wayarta ta fadi kasa, da sauri ya kai hannu ya dauko mata yana fadin,
"Kash! Sannu fa!"
Ta karbi wayar tana fadin, "Ah ba damuwa,
na gode Alhaji Faisal Zubairu!"
Idanunsa kyam a kanta ya ce, "Ashe kin san
ni?"
Ta yi murmushi ta ce, "Haba Alhaji, yadda
sunanka ya yi tambari a qasar nan ina ne ba a sanka ba? Ai duk wanda ke cikin
motar nan ma ya sanka".
Wani irin dadi ya kama shi, ya juya yana kallon
mutanen da duk suka zuba masa na mujiya, sannan ya dawo da kallonsa gare ta
yana gyada kai.
"Kwarai zancenki dutse..."
Ta katse shi da fadin, "Don Allah ko za ka
taimaka min, ka kira min shugaban kasa na fada masa, ya kamata a dinga tantance
mutane a tashar mota kada a dinga zubo 'yan Dawanau?"