Wani dan kwamitin gudanarwar babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ya zargi gwamnatin jam'iyyar APC mai mulki da hannu a rikicin da jam'iyyar ta samu kanta a ciki tsakaninta da ma'aikatanta.
Chief Olisah Metuh, sakataren watsa labarai na jam'iyyar, ya yi imanin cewa akwai wadanda ke amfani da ma'aikatan wajen kawar da hankalin jam'iyyar, sakamakon yadda take sukar abubuwan da jam'iyyar APC take yi ba dai-dai ba.
A makon da ya gabata ne dai wasu ma'aikatan jam'iyyar ta PDP suka yi bore, biyo bayan barazanar korar su daga aiki da jam'iyyar ta ce za ta yi.
PDP dai ta yi zargin cewa tsofaffin 'yan jam'iyyar wadanda yanzu suna jam'iyyar APC su ne su ka dauki mafi yawancin ma'aikatan.
Hakan a ta bakin PDP ya janyo rashin biyayya ga jam'iyyar.
Sai dai jam'iyyar mai mulki ta APC ta nisanta kanta daga abin da ke faruwa a jam'iyyar adawar.