Antaba Yin Wani Mutum Tun A Shekaru Masu Yawa Da Suka Wuce Cikin Birnin Kano A Wancan Lakaci Mai Suna Mati
Shidai Mati Wani Shahararren Matashin Manomine Wanda Duk Fadin Kewayensu Ana Jinshi
Saidai Mati Shi Mutumne Mai Matukar Son Banza DA kuma Son Kudi Tamkar Kace Tare Aka Haifeshi Da Kudi Domin Kuwa Babu Wanda Yake Ragama Akan Kudi Kodako Family Dinku Gudane Indai Ka Sake Rikicin Kudi Ya Hadaku To Ka Shiryajin Sammaci A Gidan Mai Gari Ko Kuma Wurin Yan Doka
Kwatsam Ana Nan Ana Nan Sai Allah Ya Kawo Ruwan Sama Sai Malam MATI Ya Tura Masu Shanun Huda Sukaje Suka Hudemar Rabin Gonanshi Wanda Sukakai Har Tsawon Kwana Uku Sunayi
Ammashi Malam Mati Dama Aduk Shekara Shi Kadai Yake Shuke Wannan Gona Da Kanshi Ba Tareda Ya Gayyaci Koda Yan Uwah nsa Na Jiniba Balle Abokai
Badon Komai Ba Saidon Ganin Kyashin Abunda Zai Basu
Hakanan Malam MATI Ya Dauki Buhun Irin Kyadannan Ya Daura Shi Bisa Kan Jaki Ya Nufi Gona
Da Isarsa Ya Fara Shuka Kenan Ko Kunya Daya Baiyiba Sai Yaji Ance "KAI KU TAYASHI SHUKA" nan Take Kafin Malam Yati Ya Juya Sai Yaga Kakaf Anshuke Wannan Gona Angama
Nanfa Malam Mati Ya Cika Da Farin Ciki Nandanan Shagar Gari Ya Sake Turo Ninkin Masu Shanun Huda Sukazo Landanan Suka Karasa Hude Mai Sauran Ragowar Gonan
Bayan Sun Gama Sai Maida Mlm MATI Ya Daidaici Yamma Tayi Lilis Sannan Ya Sake Daukan Wani Irin Kyada Ya Nufi Gona Da Zuwansa Shina Yana Fara Shuka Sai Yaji Ance "KAI MU TAYASHI SHUKA" Shima Kafin Ya Juyo Ya Duba Ko Waye Ke Magana Sai Yaga Har Angama Suke Gona
Shikenan Sai Lokacin Noma Yazo Shima Malam Mati Na Zuwa Ko Kunya Daya Baiyiba Sai Yaji Ance Kai Mu Tayashi "KAI MU TAYASHI NOMA" Sai Malam Mati Ya Tafi Gida Yana Murna
Sai Lokacin Hakin Kyada Yazo Bayan Tayi 'Ya'ya Tayi Komai Yazo Hakewa Yana Farawa Sai Yaji Ance "KAI MU TAYASHI HAKI" Nan Take Yaga A Hake Duka Gonan Antara Guri Guda
Bayan AnHake Basai Gogan Naku Kawai Ya Hau Tsinka Ba Ko Tushiya Guda Bai Tsinkeba Sai Yaji Ance "KAI MU TAYASHI TSINKA" Nan Take Kawai Sai Malam Mati Kafin Ya Juyo Yaga Har An Tsine Antara
To Kunsan A Ina Gizo Ke Sakar Kuwa ?
Kawai Sai Malam MATI Ya Dauki Gyada Guda Daya Ya Bare Ya Saka A Baki Kawai Sai Yaji Ance "KAI MU TAYASHI CI" Habaa Kafin Ya Juya Kawai Ba Saidai Gabaki Daya An Cinye Gyadan Saidai Tarin Bawo Habaa Nantake Sai Malam Mati Ya Yanka Ihu Tamkar Wanda Ya Zauce
hhhhhhhh hhhhhhhhh hhhhh
Amma Idan Kaine Ko Kece Hakan Ya Faruda Kai /Ke Mezakiyi ?
Kuma DON ALLAH Mekuka Fahimta Gameda Wannan Labari Shin Zafin Nemane , Ko Son Banza Takai Mlm Mati , Ko Kuma Tsautsayine ??