Da shaitanun samari da Miyagun Qawaye, ki guje musu fiye da yadda zaki guje ma kura ko zaki.. Domin hakikanin hallakar da suke tare dasu yafi na kura da zaki.
Wani lokacin zaka ga yarinya mai cikakkiyar tarbiyya amma Shaitan ya chusa mata soyayyar wani Shaitanin Saurayi.. Ta dalilin haka har sai ya lalata tarbiyyarta, ya jefata acikin ramin zina.
Wani lokacin kuma kina tare da tarbiyyar nan mai kyau wacce iyayenki da malamanki suka sha wahalar doraki akai, sai wata Qawarki ta nuna miki cewa wannan ba shine wayewa ba.. Da sannun idan baki rabu da ita ba, sai taja akalarki zuwa ga abinda zai kaiki har wutar jahannama.
Amfanin ilimi da hankali shine kayi aiki dasu wajen aikata abinda zai amfaneka da kuma guje ma dukkan abinda zai cuceka.
Duk yadda kike son mutum, indai ya fara jefo miki kalaman batsa, ko kuma yayi kokarin ta'ba jikinki, to ki rabu dashi yaje ya nemi wata mai irin halinsa... amma ba ke ba...
Ki sani cewa Duk wanda rashin kunyarsa takai har ya ta'ba jikin wacce yake fatan ta zama uwar 'ya'yansa, to hakika acikin mazinatan ma shi ba Qarami bane.
Babu wacce zata auri Mazinaci sai idan ita dinma mazinaciyar ce ko kuma Mushrika.. Hakanan babu mai aurar Mazinaciya sai Mazinaci ko Mushriki... (ALLLAH NE YA FADA, BA ZAUREN FIQHU BA).
Duk Ma'auratan da suka fara zina tun kafin aure, sun riga sun gurbata tarbiyyar Zuriyar da zasu haifa... Ya Allah ka kiyayemu don Qarfin ikonka akan bayinka.