Aure shine mafi girman al'amari arayuwar 'Ya mace. Ta hanyarsa ne zata samu damar yin cikakkiyar bauta ga Ubangijinta, sannan ta samu damar kafa nata iyalin.
Idan aure yayi jinkiri agareki, kar kiyi amfani da wannan damar wajen biyan bukatar sha'awarki ta hanyoyin da Ubangijinki ya haramta.. A'a kiyi hakuri ki kama kanki. Ki dage wajen ibadah da neman yardar Ubangijinki.
Ki kyautata zato ga Ubangijinki. Shi mabuwayi ne mai hikima. Kuma duk abinda ya Qaddara miki, to kiyi fatan Allah yasa hakan ne mafi alkhairi sannan ki nemi mafita awajensa, ba wajen bokaye da 'yan bori da 'Yan duba ba..
Zina da Ma'digo da kallon hotunan batsa, da yin chatting na batsa duk Kofofin samun tsinuwa ne da kuma fushin Ubangijinki.. Ki kyautata ma kiji tsoron Ubangijin da ya halicceki kar ki kai kanki ga Hallaka.
Idan kika aikata wani abu daga cikin wadannan, to kinci amanar kanki, Kin ci amanar Iyayenki, Kinci amanar dukkan 'yan uwanki da danginki, kinci amanar 'Ya'yan da zaki haifa nan gaba.... Sannan Uwa-Uba kinci amanar ALLAH DA MANZONSA (SAWW).
WANNAN NASIHA CE DAGA ZAUREN FIQHU, Mun rubuta ne domin isar da Sakon Allah da Manzonsa izuwa zukatan masu rabo. Allah yasa damu daku mu samu tsira aduniya da lahira. Allah shi kiyayemu daga ZINA da dukkan dangoginta. Aaameeen.
Title :
Nasiha Zuwa Ga Yan'uwa Mata Part 1
Description : Aure shine mafi girman al'amari arayuwar 'Ya mace. Ta hanyarsa ne zata samu damar yin cikakkiyar bauta ga Ubangijinta, sannan ta sam...
Rating :
5