Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ce kasar na shirin soma kera makamai domin dakarunta saboda a rage dogaro da makamai na kasashen waje.
"Mun umurci ma'aikatar tsaro ta fitar da tsari domin gina masana'antar samar da makamai a Nigeria," in ji Buhari.
Buhari ya kara da cewar zai yi wa kamfanin makamai na Kaduna watau DICON wanda aka kafa a shekarar 1964 garambawul domin soma aiki gadan-gadan.
Wata sanarwa da kakaki shugaban kasar, Garba Shehu ya fitar ta ce gwamnatin kasar za ta fitar da tsare-tsare domin ganin masana'antar ta koma ta zamani.
DICON a yanzu na kera kananan bindigogi ne da kuma wasu 'yan abubuwa na aikin farar- hula.
Dakarun Nigeria na bukatar makamai na zamani domin yaki da kungiyar Boko Haram wadda ta hallaka dubban mutane da kuma raba wasu fiye da miliyan daga muhallansu.
Title :
Najeriya Zata Fara hada Makamai
Description : Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ce kasar na shirin soma kera makamai domin dakarunta saboda a rage dogaro da makamai na kasashen waje. ...
Rating :
5