Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci manyan hafsoshin dakarun kasar su kawo karshen kungiyar Boko Haram a cikin watanni uku.
A lokacin bikin rantsar da manyan jami'an tsaron kasar, Buhari ya ce lokaci yayi da za a kawo karshen kungiyar Boko Haram wacce ta hallaka dubban mutane a cikin fiye da shekaru shida.
"Dole ne ku zage damtse, kuma mu ci gaba da aiki da sauran masu ruwa da tsaki domin kawo karshen masu tayar da kayar baya a cikin watanni uku," in ji Buhari.
Ya kara da cewar, "Ya zama wajibi ku kare fararen hula da kuma mutunta hakkin abokan hammaya."
Manyan Hafsohin sojin sun hada da Major-General Abayomi Gabriel Olonishakin da Major-General T.Y. Buratai da Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas da kuma Air Vice Marshal Sadique Abubakar.
Tun da aka rantsar da Buhari a matsayin shugaban Nigeria a karshen watan Mayu, kungiyar Boko Haram ta hallaka mutane kusan 900.
A karshen watan Yuli ne rundunar hadin gwiwa kan yaki da Boko Haram mai dakaru 8,700 ta soma aiki.
Rundunar ta kunshi sojoji daga Nigeria da Niger da Kamaru da Chadi da kuma jamhuriyar Benin.
Title :
"Na ba ku wata uku ku gama da Boko Haram"
Description : Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci manyan hafsoshin dakarun kasar su kawo karshen kungiyar Boko Haram a cikin watanni uku. A lokacin bikin...
Rating :
5