A Najeriya mutane 7 ne suka rasa rayukansu a kaduna bayan da wani jirgin soja mai saukar angulu ya fadi jim kadan bayan tashinsa.
Jirgin Kirar Donier 228 na rundunar sojin saman kasar yana kuma dauke da mutane 7 ne wadanda suka tashi daga filin jiragen saman sojojin kasar dake Kaduna.
Babban hafsan mayakan samar Nigeria, Air Marshall Saddiq Abubakar, wanda ya katse wata tafiya zuwa Fatakwal, domin ziyarar wurin da abun ya faru, ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano musabbin hadarin.
Rahotanni sun ce jirgin ya fadi ne a gab da wani gida a tsohuwar NDA a garin na Kaduna.
Title :
Mutane 7 ne suka rasu a Kaduna
Description : A Najeriya mutane 7 ne suka rasa rayukansu a kaduna bayan da wani jirgin soja mai saukar angulu ya fadi jim kadan bayan tashinsa. Jirgin Ki...
Rating :
5