Rahotanni daga birnin Maiduguri a jihar Borno sun ce mutane uku suka hallaka yayin da mutum daya ya jikkata a harin kunar bakin wake da wasu matasa biyu suka kai a wurin gudanar da bincike a Airport junction.
Rahotanin dai sun ce lamarin ya faru ne a jiya Talata da daddare lokacin da dokar hana zirga-zirga ta soma aiki .
Sun kuma ce matasan sun ta da bam din ne lokacin da sojoji suka hanasu shiga cikin birnin Maiduguri.
'Yan kunar bakin waken da kuma soja guda na cikin wadanda suka rasa rayukansu yayin da wata yarinya ta ji raunuka.
An kai harin ne bayan wanda wasu 'yan kunar bakin-wake suka kai a garin Damataru a ranar Talata.
Title :
Mutane 3 sun hallaka a birnin Maiduguri
Description : Rahotanni daga birnin Maiduguri a jihar Borno sun ce mutane uku suka hallaka yayin da mutum daya ya jikkata a harin kunar bakin wake da wasu...
Rating :
5