Asalin addini a duniya shi ne musulunci. Mutum na farko da Allah ya halitta, [[Annabi Adam]] (alaihis salam), ya rayu ne bisa tafarkin musulunci. Dukkanin manzanni tun daga [[Annabi Nuhu]] (alaihis salam), zuwa [[Annabi Ibrahim], da [[Annabi Musa]], da [[Annabi Isa]], alaihimus salam, musulmai ne ma su kadaita Allah. Sai dai gaba dayansu Allah ya aikosu ne zuwa ga al'ummominsu kadai.
Annabi na karshe kuma cikamakin tsarin annabawa shi ne Annabi Muhammadu (yabo da amincin Allah su tabbata a gareshi). Allah ya aiko Annabi [[Muhammad]]u (SAW) da sako zuwa ga daukacin al'ummar duniya, mutane da aljannu. An haifeshi a birnin Makkah da a yanzu ke kasar Saudi Arabia. Annabi Muhammadu (SAW), bakureishe ne, dan Abdullahi da Amina daga tsatson Annabi Isma'ila (AS) dan Annabi Ibrahim (AS).
Shika Shikan Musulunci
Shika shikan Musulunci guda biyar (5) ne kamar haka : Kalmar shahada (TAUHIDI), Sallah, Azumi, Zakkah, da Aikin hajji ga wanda ke da iko.
===Kalmar Shahada===
Ma'anarsa shine shaidawa babu abun bauta bisa cancanta sai ALLAH (SWT), sa'annan Annabi [[Muhammad]] (SAW) Manzon Allah ne.
=== Sallah ===
Sallah yana daga cikin shika shikan Musulunci mai mahimmanci matuka bayan Tauhidi, ana bukatar kowanne musulmi yayi Sallah sau biyar a rana, yana mai fuskantar [[Ka'aba]] dake kasar [[Saudiya]]. A kasashen Musulmai, za'a ke jin Kiran Sallah daga [[Masallaci]] mafi kusa a yayin da lokacin Sallah yayi. Sallah ana yinta ne cikin Natsuwa, domin a samu kyakkyawan lada.
=== Azumi ===
[[Azumi]]: Wannan rukuni ne wanda ake nufin barin ci, da sha, da yin jima'i daga fitowan alfijir har zuwa faduwan rana. Dukkan musulmi tilas ne da ya/ta azimci watan Ramalana (watau wata na tara a kalandar musulunci).
=== Zakka ===
Shine cire wani kayyadadden kaso, daga cikin wasu kayyadaddun dukiyoyi, a cikin wani kayyadadden lokaci ga wasu kayyadaddun mutane, domin Allah (SWT).
=== Hajji ===
Shine zuwa ziyartan dakin Allah Mai Alfarma ga wanda keda iko da nufin Ibada.
=== Imani ===
Ma'anan Imani shine : abun da zuciya ta kudurta, harche yayi furuci da shi, sa'annan gabban jiki suka yi aiki da shi. Imani yana da shika-shikai guda shida (6) kamar haka : Imani da Allah, da Mala'ikunsa, da littafansa, da Manzanninsa, da Ranar karshe, da Imani da kaddara mai dadi ko marar dadi.
Title :
MENENE MUSULUNCI?? - Tarihin Addinin Musulunci
Description : Asalin addini a duniya shi ne musulunci. Mutum na farko da Allah ya halitta, [[Annabi Adam]] (alaihis salam), ya rayu ne bisa tafarkin mu...
Rating :
5