Gwamnatin jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Nigeria ta bullo da wani sabon tsari na bayar da hutun makwanni uku ga maza ma'aikata idan matansu sun haihu.
Gwamnatin dai ta ce hakan wani mataki ne da jihar ta dauka na ba wa mazajen dama domin su taimaka wa matan nasu yadda ya kamata.
Su ma mata ma'aikatan jihar an ware musu hutun watanni shida idan sun haihu, sabanin watanni uku da ake gwamnatin tarayya da wasu jihohi suke bayarwa.
Ba kasafai ne dai ake bayar da irin wannan hutu na haihuwa ga maza ma'aikata a Najeriya ba.