Imamuz Zuhriy (daya daga cikin manyan magabata) ya ruwaito daga Asma'u bintu Rahmin, ita kuma taji Mahaifiyarta tana cewa:
"Na halarci wajen Aminatu (mahaifiyar Annabi -saww-) alokacin rashin lafiyarta wacce ta rasu acikinta. Alokacin nan shi Annabi Muhammadu (saww) yana Qaramin yaro kimanin shekara biyar (amma shekara 6 tarihi ya nuna). yana tsaye kusa da kan ta.
Sai ta dubi fuskarsa sannan ta fadi wasu baitukan Waqa, sannan tace:
"DUKKAN RAYAYYE MATACCE NE. KUMA DUKKAN SABON ABU, WATARANA ZAI TSUFA. KUMA DUKKAN WANI ABU MAI YAWA WATARANA ZAI QARE.
"NI YANZU ZAN RASU, AMMA AMBATONA ZAI WANZU, DOMIN HAKIKA NI NA BAR ALKHAIRI, KUMA NA HAIFI MAI TSARKI".
Ta gama fadin wannan kalmomin sai ta rasu.
Kuma akwai ruwaya daga Sayyidah Aisha (ra) - Suyutiy ya inganta hadisin acikin TA'AZEEM WAL MINNAH - tana cewa:
"Manzon Allah (saww) ya sauka a "HAJOUN" (Sunan wani waje ne) yana cikin bakin ciki da damuwa, ya zauna awajen har yadda Allah yaso. Sai kuma ya dawo yana farinciki yana murna.
Sai yace : "NA ROKI UBANGIJINA NE, YA RAYA MIN MAHAIFIYATA TAYI IMANI DANI SANNAN YA MAYAR DA ITA".
Hakanan Suhaily da Khateeb Albaghdadiy duk sun ruwaito hadisi daga Nana Aisha (ra) wanda aciki ta kawo maganar cewa ALLAH YA RAYA MASA IYAYENSA KUMA SUNYI IMANI DASHI.
Hadisin da yake magana akan cewa wai iyayensa suna wuta, an ruwaitoshi ne ta hanyar Hammadu bn Salamah, kuma hadisin bai inganta ba.
Anan nake jan hankalin 'Yan uwa Musulmai ku sani cewa Fadin mummunar magana akan Mahaifan Manzon Allah (saww) chutarwa ne gareshi. Kuma duk wanda ya chuchi Manzon Allah (saww) to ya chuchi Allah. Kuma Allah yana cewa:
"HAKIKA WADANNAN DA SUKE CHUTAR DA ALLAH DA MANZONSA, TO ALLAH YA TSINE MUSU ADUNIYA DA LAHIRA, KUMA YA TANADAR MUSU DA WATA IRIN AZABA MAI WULAKANTARWA".
(Suratul Ahzab ayah ta 57).
A karkashin wannan ayar, Ibnu Katheer ya kawo hadisi daga Abdullahi bn Abbas (ra) yana cewa:
"WANNAN AYAR TA SAUKA NE SABODA WADANDA SUKA SOKI LAMARIN MANZON ALLAH (SAWW) AKAN AURENSA DA SAFIYYAH BINTU HUYAY (RA).
Amma a zahiri wannan ayar ta hada gaba daya da duk wanda ya chutar da SHI (SAWW) da wani abu. (komai kankantarsa).
Kuma duk wanda ya chutar dashi, to ya chutar da Allah. kamar yadda duk wanda yayi masa biyayya, to yabi Allah ne..
'YAN UWA GA TAMBAYA : Shin duk wanda ya fadi mummunan kalamai akan Mahaifan Manzon Allah (saww) ya chucheshi, ko bai chucheshi ba???
- Masu fadin cewa "wai" kafirai ne, shin yaya zakuyi da Sahihin hadisin nan da Manzon Allah (saww) wata aje cewa: "NI ZABABBE NE DAGA ZABABBU, DAGA ZABABBU, DAGA ZABABBU".
Shin Allah yana za'bar kafirai ne ya fifitasu akan Muminai, har ma ya sanya hasken Annabinsa ajikinsu???
- Tunda Allah ya tsine ma wadanda suka Soki maganar aurensa, Harma ya tanadar musu da wata irin azaba mai wulakantarwa, to yaya kuma wadanda suka soki iyayensa??
Kwanakin baya na kawo maganganun Mqnyan Maluman Musulunci akan cewa DUK WANDA YA CHUTAR DA MANZON ALLAH (SAWW) TO KAFIRI NE. WANDA YAYI KOKONTO CIKIN KAFIRCINSA MA KAFIRI NE.
'Yan uwa ya kamata mu tsarkake Imaninmu. Ba zaka zama cikakken Mabiyin Sunnar Manzon Allah (saww) ta hakika ba, har sai kana ganin girmansa da mutuncin da Soyayyarsa fiye da dukkan Kowa da komai.