Assalamu alaikum warahmatulahi wabarakatuh.
Malam Allah yakare mana kai, ya saka maka da Iyayenka da Aljannah.
Kanwatace ta kasance abaya can tasami matsalan rashin bacci da ciwon kai har saida sukaje psyciatric.
Tana makaranta sai aka mata aure (anyi dauki ba dadi kafin ayarda da wanda takawo, wanda wannan yasata a damuwa sosai kafin Allah yakawo karshen abin). Rananda za'a kaita gidan miji sai kawai tafara cije cije da ihu dasauransu, kamar mai hauka. Malaman ruqyah sunce asirine aka mata, bashida alaka da jinnul aashiq. Ta taba samun matsala dawasu yan mata a makaranta (university), wanda zamanta dasu yajanyo mata damuwa mai yawan gaske, kasantuwarta ustaziya (su kuma ma ana tunanin yan secrete soceity ne).
Alhamdulillah, tasamu lafiya kuma har tahaihu biyu. Nafarkon ba matsala, amma bayan tahaihu nabiyu lafiya kalau da yan kwanaki (kafin suna) sai kawai tasamu rikicewar kwakwalwa (wanda wani mai ruqya yace ba matsalar jinnu bane, wai na asibitine).
Riki cewar kwakwalwar acewar mahaifiyramu yasamo asaline daga maganganu masu zafi da mijinta taa iya yuwuwa yafadi mata (wanda watakila akwai barazanar saki aciki) saboda wani request da mahaifiyarmu tayi na cewa ya kamata ayi sulhu tsakanin shi mijin da kishiyar mamana (ansami sabaninne saboda shi ya yarda dacewa itace tayi mata asiri kamar yanda jinnun suka fadi, wanda mu bamu yardaba tukunna saboda har yau Allah bai bayyanarda hakanba, kuma kasantuwarmu munada saiti, kada kahan yakawo mana matsala a zamantakewarmu).
Munje psychiatric an bata magunguna, amma da alamun warakar sai ahankali.
Kwanaki naga kayi post a facebook akan rikicewar kwakwalwa. Maganine da ake hadawa da ALMUJARRAB da zaitul lauz. Shin wannan maganin zai iya taimakawa ko ko akwai wani taimako na daban da malam zaiyi mana.
Allah ya bada lada, ya albarkaci zuriyya, ya gafarta wa iyaye, kuma yayi sakayya maka da iyaye da Aljanna.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh. Hakika wannan 'yar uwar taka ta hadu da manyan matsaloli sosai. To amma babbar matsalar tana cikin yardar da kukeyi da Qarya irin ta Aljanu.
Aljanu mafiya yawansu MAKARYATA NE kamar yadda Ubangiji ya bayar da shaida akansu. Don haka bai kamata ku yarda da duk abinda zasu gaya muku ba.
Wani lokacin idan Aljani ya riga ya raina muju wayo ba zai taba fitowa ya gaya muku gaskiya ba. Zai iya yi muku duk kowacce irin Qarya domin ya samu nasarar gusar da tunaninku daga kan ainihin larurar da shi Aljanin yake haifarwa ga marar lafiyar.
Kar ku yarda da batun da sukeyi cewar wai aikosu akayi. Ku dai ku dogara ga Allah kuci gaba da bin hanyoyin da suka dace domin samun lafiyarta.
Su da kansu zasu iya rikitar mata da tunaninta, su dauke mata hankalinta, kuma su sanya mata Miyagun kalmomi abakinta yadda zata iya gaya ma kowa bakar magana. (Wannan kadan ne daga cikin irin sharrinsu).
Ku Dora ta busa hanyar Karatun Alqur'ani da nacewa wajen Zikirin Allah akoda yaushe bayan azkar na safe da yamma da sauran zikirori.
Ku samu shi Almujarrab din da wani Brain Tonic (shima ana samunsa awajenmu) Sannan ku hada da MUHRIKUL JINNI na shafawa. Da kuma sauran magungunan da suka dace.
Allah ya sawwake, Allah ya bata lafiya. WALLAHU A'ALAM.