Gwamnatin Jihar Borno ta sanar da rasuwar Mataimakin Gwamnan jihar, Alhaji Zannah Umar Mustapha.Mataimakin Gwamnan ya rasu ne yau da asuba a Yola, babban birnin jihar Adamawa, inda ya je wakiltar Gwamnan Borno a wajen bikin yaye daliban jami'ar fasaha ta Modibbo Adama.
Wata sanarwar da ta fito daga fadar gwamnatin ta ce za a jana'izar marigayin idan an jima da maraice, a fadar gwamnatin da ke Maiduguri.
Tuni dai gwamnan jihar Bornon, Alhaji Kashim Shettima ya bayyana alhini dangane da wannan rashi, yana adu`ar Allah ya gafarta masa.
Title :
Mataimakin Gwamnan Borno ya rasu
Description : Gwamnatin Jihar Borno ta sanar da rasuwar Mataimakin Gwamnan jihar, Alhaji Zannah Umar Mustapha.Mataimakin Gwamnan ya rasu ne yau da asuba a...
Rating :
5