Manchester United ta tuntubi Southampton kan ko za ta sayar mata da Sadio Mane dan kwallon tawagar Senegal.
Tun a makwon jiya ne United take ta kokarin karo dauko dan wasa kafin a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan kwallon kafa.
Dan kwallon da United ta dade tana zawarci Pedro daga Barcelona ya juya akalarsa a inda yake daf da saka hannu a kungiyar Chelsea.
Mane ya ci kwallaye 10 a wasanni 32 da ya yi a bara a Southampton, tun komawarsa kulob din daga Red Bull Salzburg na Austria kan kudi £10m.
Title :
Manchester United ta taya Sadio Mane na Southampton
Description : Manchester United ta tuntubi Southampton kan ko za ta sayar mata da Sadio Mane dan kwallon tawagar Senegal. Tun a makwon jiya ne United tak...
Rating :
5