Wani mai magana da yawun majalisar koli ta 'yan Talliban dake Afganistan ya fadawa manema labarai cewa ba a tuntube su ba, a zaben jagoran kungiyar da aka gudanar a kwanan nan, bayan mutuwar shugaban kungiyar Mullah OMar
Mai magana da yawun majalisar Mullah Abdul- Manan Niazi, ya ce majalisar zata gudanar wani Taro a yanzu, domin zabar sabon Shugaba
A ranar Alhamis ne majiyoyin kungiyar Taliban suka ce an zabi Mullah Mansur a matsayin sabon jagoran kungiyar
Wasu fitattun kungiyar Taliban sun soki wasu masu goyan- bayan Pakistan da tilasta shugabancin Mullah Mansur akansu