Kwamitin Sulhu na Majalisar dinkin duniya ya gargadi Gwamnatin Sudan ta kude cewa zai dauki mataki mai tsauri a kan ta muddin ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar kasar a wannan larabar.
Shugabar kwamitin kuma Jakadiyar Najeriya a Majalisar, Amsada Joy Ogwu ta bayyana matsayin daukacin kasashen da ke Majalisar na tabbatar da cewar Shugaba Salva Kiir ya sanya hannu kan yarjejeniyar kamar yadda ya yi alkawari.
Kara wasti da batun cim ma yarjejeniyar zaman lafiya zai sanya majalisar kakabawa gwamnatin Sudan ta kudu takunkumi.
A na dai saran shugabanin kasashen Kenya, Uganda, Sudan da Habasha su halarci zaman sanya hannun.
Akalla kashe 70 ciki 100 na al’ummar sudan ta kudu ne ke fama da rashin abinci, yayin da sama da fararan hula dubu 200 ke mafaka a sansani dakarun Majalisar dinkin duniya sakamakon rikicin kasar.
Title :
Majalisar dinkin duniya ta yiwa Sudan ta kudu gargadin karshe
Description : Kwamitin Sulhu na Majalisar dinkin duniya ya gargadi Gwamnatin Sudan ta kude cewa zai dauki mataki mai tsauri a kan ta muddin ta ki sanya ha...
Rating :
5