Kwamitin majalisar dattawan Nigeria zai binciki shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Lamorde bisa zargin karkatar da biliyoyin daloli.
Ana zargin shugaban EFCC da wasu jami'an hukumar da zargin karkatar da kusan naira tiriliyon daya wadanda aka kwato daga hannun mutanen da aka samu da laifin handame kudaden al'umma.
Ana saran a wannan makon, Lamorde zai bayyana gaban kwamitin da'a na majalisar dattawan domin ya kare kansa.
Matakin na zuwa ne 'yan makonni bayan da hukumar EFCC ta gayyaci uwargidan shugaban majalisar dattawan watau Toyin Bukola Saraki domin ta amsa tambayoyi kan zargin aikata ba daidai ba.
Wasu masu sharhi a kan al'amuran yau da kullum a Nigeria na zargin cewar matakin majalisar ba zai rasa nasaba da siyasa ba.
Wani mai kamfanin tsaro a Nigeria, George Udoh ne ya gabatar da zarge-zargen kan hukumar ta EFCC ga majalisar dattawan, abin da ya sa ta ce za ta bincika.
An ambato 'yan jam'iyyar adawa ta PDP a majalisar dattawan na cewar a irin wannan lokacin bai dace a gudanar da bincike kan shugaban EFCC din, Ibrahim Lamorde ba.
Title :
Majalisar dattawa za ta binciki Lamorde
Description : Kwamiti n majalisar dattawan Nigeria zai binciki shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Lamorde bisa zargin karkatar da biliyoyin daloli. Ana zargi...
Rating :
5