i‘Sai Mai rusau,’ Wannan shi ne kirarin da ake yi wa Malam Nasiru El-Rufa;i lokacin yakin neman zaben zama gwamnan jihar Kaduna. Sai dai kuma a lokacin ana fadin haka ne cikin raha, shi kansa Gwamna El-Rufa’i yana yi kansa kirari da hakan, inda ya kan ce, ‘ ku zabi mai rusau ya rushe PDP.’
Sai dai kuma a shekaranjiya Laraba gwamnatin Malam Nasiru El-Rufa’i ta fara rushe gine-ginen da aka yi a harabar Kwalejin Alhudahuda da ke Zariya da nufin ceto filayen makarantun jihar daga mamayewa.
Gwamna El-Rufa’i ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta da niyyar rushe-rushe, amma za ta rushe duk ginin da aka yi a filayen makarantu da asibitocin da ke fadin jihar Kaduna. Kuma ta kuduri aniyar haka babu ja da baya.
Mai bai wa Gwamna El-Rufa’i shawara kan harkokin addini, Injiya Namadi Musa ya bayyana a wata hira da gidan Rediyon Nagarta da ke Kaduna ya yi da shi cewa, gwamnati ta dauki wannan matakin ne domin amfanin al’ummar jihar, kuma ‘’ idan abin da muke yi ba don Allah ba ne, Allah Ya karya mu.’’
Shugabar Hukumar kula da tsarin manyan garurruwan jihar Kaduna (KASUPDA) Misis. Saratu Haruna ta ce wannan matakin da gwamnati ta dauka na rushe gidajen da ke harabar kwalejin Alhudahuda cika alkawarin da ta yi ne na rusa gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba, kuma wadanda suka yi gini a harabar makarantun gwamnati dama mun ba su wa’adi na makonni uku, wato zuwa ranar 3 ga wannan watan, cewa duk wanda bai rusa ba, to mu za mu rusa kuma ya biya kudin rusawa. To wa’adin ya cika, don haka muka zo don mu rusa da kanmu, kuma aiki na tafiya yadda ya kamata.
‘Yadda muka mallaki filayen’
Wadanda suka yi gini a cikin harabar kwalejin Alhudahuda da ke Zariya a jihar Kaduna sun bi umurnin da Gwamna Nasiru El-Rufa’i ya bayar na cewa su kwance gine-ginen da suka yi nan da makonni uku ko kuma gwamnati ta rusa.
Lokacin da Aminiya ta ziyarci harabar kwalejin ta tarar da mutane suna ta kwashe kayayyakinsu daga gidajensu suna kuma rusawa, kamar yadda aka ba su umurni.
Wani magidanci mai suna Aliyu Adam, ya bayyana wa wakilinmu cewa, ``asalinmu daga garin Kachiya ne na jihar Kaduna, a shekara ta 2000 rikicin da aka yi a jihar Kaduna ya shafe mu, inda aka kashe mana iyaye da `yan uwa kuma aka bata mana dukiya, aka kona mana gidaje, hakan sai ya zama sanadiyyar yin hijirarmu muka dawo Zariya da zama, bayan lokaci kadan Allah Ya hore wa yayana ya nemi amininsa da ya nema masa fili domin ya saya, kuma aka nema masa fili a wannan wurin da kake gani. Kuma bayan bincike da muka yi an tabbatar mana da cewa wannan fili nasa ne ba na wani ba, kuma an nuna mana cewa ga iyakar filin da makaranta ta mallaka. To abinka da wanda bai sani ba kuma yana neman inda zai rufa wa kansa asiri, don haka muka saya muka biya, muka gina,muka tare.To an wayi gari yau an ce mu kwance ginin mu kuma rusa da kanmu, to ka ga wannan ai jarabawa ce daga Allah. Dama mun dade muna fama da wahalhalu daban-daban sai ran da Allah Ya kawo mana karshensa.’
Sai dai ina kira ga wannan gwamnati da muke wa kyakykyawan zato da ta bincika ta tace domin ta yi adalci akan mu da wannan abu ya shafa. Domin kuwa mu har sai da aka nuna mana wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban makarantar cewa wannan fili ba na makarantar ba ne, gashi kuma mafiya yawanmu talakawa ne ba wani mai kawo mana dauki a kan wannan lamari, daga Allah sai su din nan da suka ce mu tashi.’
Haka kuma Aminiya ta ji ta bakin wani dattijo wanda ya shafe shekara talatin a wannan Unguwar da ke kusa da harabar, inda ya ce, ``sunana Yahaya Ayuba, kuma yanzu akalla ina da shearu 75 kuma ni malamin makaranta ne, wannan abu da ya same mu tare da `yan uwana mazauna wannan unguwar, mun sani jarabawa ce daga wurin Allah, domin ita wannan jayayya an taba yenta, don haka ya sa a matsayina na dattijo mazaunin wannan unguwa muka hadu da hukumar makaranta tare da wakilan sarakuna aka fitar da iyakar da ake zaton na makarantar ne, sannan aka yi a rubuce. Shi shugaban makarantar na wancan lokaci mai suna Bashir Aliyu ya sa aka bi duk aka fitar da iyak kar da ake zaton na makarantar ne, sannan aka yi a rubuce. Shi shugaban makarantar na wancan lokaci mai suna Bashir Aliyu ya sa aka bi duk aka fitar da iyakar makarantar, sannan ya ba mu takarda a rubuce wanda take dauke da kwanan watan 08/07/11, tare da sa hannunsa, sannan aka kewaye makarantar baki daya. Wanna shi ne abin da muka sani, don haka inda muka yi gidajenmu ba harabar makaranta ba ne. Don haka ina kira ga wannan gwamnati ta tuna cewa muna murna ne cewa mun baro wahala a baya, bai kamata ba tun yanzu a fara dandana mana daci ba kafin dadi. A tarbiyance kodayaushe ana so ne ka fara jiyar da dadi ga wadanda kake shugabanta, idan sun ki bi to sai ka jiyar da su daci domin su gyara.’’
Wani tsohon malami a kwalejin Alhudahuda, Dakta Muktar Ibarahim Maccido, wanda a yanzu shi ne shugaban tsohuwar Kwalejin ilimi mai zurfi ta Zariya (FCE), ya nuna goyon bayansa a kan matakin da Gwamna Nasiru El-Rufa’i ya dauka na maido da martabar ilimi tare da iganta makarantu a jihar, ya ce, `a kwalejin Alhudahuda a shekarar 1986 zuwa 1989 mu ne muka fara fada da wani a lokacin da ya shigo filin makarantar ya fara gina rukunin gidaje, mu kuma muka fito muka nuna rashin yardarmu a kan hakan, ana cikin haka ne na bar makarantar na koma jami’a. To wanna shi ne musabbabin da wadansu suka samu kofar shiga makarantu, don haka ni ina goyon bayan kwace duk wani fili da ya shafi harabar makaranta.’’
Duk kokarin da Aminiya ta yi domin jin ta bakin masu unguwanni da sarakuna ya ci tura, domin kuwa sun nuna cewa ba za su iya cewa komi ba.
Title :
‘Mai rusau’ ya fara aiki a Zariya
Description : i ‘Sai Mai rusau,’ Wannan shi ne kirarin da ake yi wa Malam Nasiru El-Rufa;i lokacin yakin neman zaben zama gwamnan jihar Kaduna. Sai dai ku...
Rating :
5