Shugaban Chadi, Idriss Deby ya ce kungiyar Boko Haram ta samu sabon shugaba.
Mista Deby bai bayyana abin da ya faru da Abubakar Shekau ba, amma ya ce an maye gurbinsa da Mahamat Daoud.
A 'yan watannin nan kungiyar Boko Haram ta fitar da bidiyo inda bata nuna Shekau ba, abin da ya sa ake tunanin ko an kashe shi ne.
Idriss Deby ya bayyana Boko Haram a matsayin kungiyar da aka ci galabarta, kuma wannan sabon shugaban Mahamat Daoud a shirye yake ya yi sulhu da gwamnatin Najeriya.
A shekarar da ta wuce, shugaban Chadi ya nemi shiga tsakani domin a yi sulhu da Boko Haram.
Rabon da a ji duriyar Shekau tun a watan Maris, inda ya fitar da sakon yin mubaya'a ga kungiyar IS mai ikirarin kafa daular Musulunci.
A wani bidiyo da Boko Haram ta fitar a farkon wannan watan, an ga wani matashi da ya yi magana da Hausa, amma bisa alamu dan kabilar Kanuri ne kamar Shekau.
A cikin watan Maris na bana, Shugaba Deby ya yi ikirarin cewa sun san inda Shekau ya boye.
"Idan Abubakar Shekau na son kansa da lafiya, to ya mika wuya, mun san inda yake. Idan bai mika wuya ba, makomarsa za ta zama iri daya da sauran mabiyansa," in ji shugaba Deby.
Mutane fiye da 15,000 ne suka rasu tun da aka soma rikicin Boko Haram a Nigeria.
Title :
Mahamat Daoud shi ne sabon shugaban Boko Haram - Deby
Description : Shugaban Chadi, Idriss Deby ya ce kungiyar Boko Haram ta samu sabon shugaba. Mista Deby bai bayyana abin da ya faru da Abubakar Shekau ba, ...
Rating :
5