Assalamu alaikum malam dan girman Allah ina son a taimaka min kamar yadda Allah ya taimakeka akan mahaifiyata dani kaina.
dafarko dai malam inaimaka fatan alkairi dakai da iyalanka da jama ar wannan zaure baki daya dafatan Allah ya kare manakai kuma ya jiqan mahahaifanka gaba daya.
malam yau mahaifiya shekara daya da rabi kenan tana fama da mutuwar barin jiki( strock ) munyita kokarin yin magani har yanzun Allah bai sa an dace ba sannan muna cikin wannaan hali ga lafiya tayi qaranci a gareta yau complain ciwon kai ciwon qirji ciwon haqarqari ko kuma ta ce bata gani zuwa dan wani lokaci sai ganin ya dawo sannan ga yawan mantuwa yanzun nan zakuyi magana da ita amma inka dawo zatace bata taba magana da kai ba ita ta manta. abu na qarshe kuma shine wani lokaci sai taji hannun ta kamar zata iya motsashi amma da ta fadama mani ko kuma wani sai taji wani abu yayi shocking dinta a cikin hannun sai ta fara yin wani abu kamar me farfadiya tai ta shureshure sai an rirriqeta ayitamata tofi sannan ya sake ta wlh duk ranar da tayi irinhaka to wlh dani da ita duk babu mai iya yin barci ita sbd tsoro nikuma sbd batayi bacciba haka zamu kwana sannan jikinta sai ya sake komai ba zata iyayi ba sai ammata kai ko tashi sai an tasheta awannan yini dan Girman Allah ka taimaka min da abinda Allah ya hore maka na magani da addua daga gareka da jama ar wannan zaure.
sannan malam matsalata shine yawan ciwon kai da kuma yawan bacin rai sannan basir dake yawan damuna idan naci abu mai yaji wlh malam bana iyazama kuma haka kawai sai ramewa nake yi mutane suke cemin wai basir dinne yake sani rama dan Allah malam ataimaka min sbd Allah
daga Surajo Abdullahi.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Hakika shi Stroke yana daga cikin manyan chututtuka masu nauyi sosai. Muna fatan Allah ya kawo sauki, ya bata ladan jinya, kai kuma Allah ya baka ladan biyayyar Mahaifa.
Daga cikin manyan abubuwan da suke taimaka ma mai irin wannan jinyar, ga wasu abubuwan da na rairayo maka:
Shi dai stoke/paralysis yana faruwa ne sakamakon toshewar hanyoyin shiga da fitar Jini wadanda suke jikin Zuciyar 'Dan Adam. Su kuma suna toshewa ne ta dalilin ginuwar kitse marar amfani acikinsu, da kuma samuwar matattun kwayoyin halitta (cells) idan suka taru acikin hanyoyin jijiyoyin.
1. QAHO : Yin Qaho irin na Wanzamai yana daga cikin manyan hanyoyin da Musulunci ya yarda abisu dimin samun lafiyar jiki.
Manzon Allah (saww) yace: "WARAKA TANA CIKIN ABUBUWA GUDA UKU: ZUMA, QAHO, DA KUMA SAKIYA. AMMA NA HANA AL'UMMATA YIN SAKIYA".
(Ibnul Qayyim acikin Littafinsa Tibbun Nabawiy).
Binciken Likitocin Musulunci ya tabbatar da cewa yawaita yin Qaho yana fitar da mataccen Kwayoyin jini daga jikin Dan Adam. kuma yana bude kofofin harbawar jini zuwa cikin zuciya. Kuma yana daidaita bugawar zuciyar mutum. Don haka koda Masu hawan jini idan suna yin Qaho jininsu zai rika sauka cikin sauki.
Hakanan masu fama da Paralysis ko Stroke su ma zai musu amfani sosai.
2. ZOGALAI DA KABEJI: Asamu danyen ganyen zogalai kamar cokali 7, Asamu Kabeji mai kyau ayanyankashi asamu cokali 7 dinsa.
Awankesu sosai gaba dayansu sannan azuba cikin blender tare da ruwan zobo kofi biyu a markadasu. Sannan a sanya rariya a tace ruwan. Azuba zuma arika sha.
In sha Allahu wannan zai yi amfani sosai ga masu fama da shanyewar jiki, ko masu Sickle cell anaemia (SIKILA) Da masu hawan jini, da masu Ulcer, da masu ciwon tari (Kamar Asthma) da sauransu.
3. Ka samu Shayin Almujarrab na ZAUREN FIQHU ka dafa cokali 2 acikin ruwa kofi guda. Idan ya dahu ka tache sannan ka sanya Man Habbatus sauda (na kampanin Hemani) cokali guda aciki, sannan ka bata ta rika shansa har ya Qare.
In sha Allahu zakayi mamakin saukin da za'a samu. Domin kuwa tunaninta zai dawo daidai, kuma Hanyoyin jininta zasu bude sosai yadda gabobinta zasu rika motsawa da izinin Allah.
4. Hanya ta hudu kuma ka samo Man Zaitun mai kyau (Virgin Olive Oil) a karanta Fatiha 7, Ayatul Kursiyyi 7, Qul Huwallahu da falaki da naasi su ma 7. Ayatush shifa'i ma ha ka.
Wannan man Zaitun din shine zata rika shafawa ajikinta ko yaushe. Kuma bayan ta shafa din sai ta fito cikin hantsi ta zauna kamar minti 10 - 15.
Kuma ta rika cinsa acikin abinci.
In Allah ya yarda zata samu lafiya.
ALLAH YASA A DACE.
WALLAHU A'ALAM.