mallam da mafificin alkhairi bisa taimakon da kake wa al'ummar Annabi s.a.w game da abinda ya shige mana duhu na addini da ma na lafiyar mu. Mallam don Allah taimako nake nema, Mata ke fama da kaikayin gaba, a da ciwon Mara ke yawan damunta amma yanzu ya dena sai kaikayin gaban kuma tana complain cewa wannan yar fatar ta cikin farjin ta ke kaikayin, gashi kuma tana da ciki wata 5, amma mallam tun da nake da ita ban taba jin dadin saduwa da ita ba sai nazo yin inzali nake ji. Mallam ataimaka don naga ta fara shiga damuwa. Sannan kuma mallam ina bukatar shawarwi game da abubuwan da ya kamata in hada mata don karin lafiya gareta da jaririn dake cikinta. Nagode Allah Ya jikan mahaifa.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh. Matsalar kaikayin gaba yawancin mata da yawa suna fama dashi, kuma yana da dalilai masu yawa da suke kawoshi.
MISALI KAMAR:
1. Rashin Tsaftace wajen ko askeshi akan kari.
2. Yawan yin tsarki da ruwan sanyi marar tsafta.
3. Sanya wando mai damshi.
4. Wanke gaba da sabulu.
5. Shan magunguna wadanda ba'a tabbatar da sahihancinsu ba.
7. Matsalar Shafar Aljanun Soyayya (JINNUL ASHIQ).
Yawancin lokaci irin wannan larurar tana da wuyar magani agun likitocin Zamani. Musamman ma idan Aljani ke kawota. Dole sai anyi maganin Aljanin, an kamashi a umurceshi ya dauke ajiyar da yayi awajen.
Amma dai koma menene musabbabin abun, ga wasu magunguna nan masu inganci a jarraba. in sha Allahu za'a dace:
1. APPLE VINEGAR (KHAAL TUFFAH) : Arika hadashi da ruwan dumi ko kuma hakanan yadda yake, ana chuda wajen, anan watsawa sosai.
2. INGANTACCEN GARIN HULBA : Arika dafawa cokali 3 ruwa kofi biyu, ahada da cokali biyar na Khal Tuffah ko farin Khal (White Vinegar). Idan ya dahu sannan a surka ruwan arika shiga ciki ana dumama wajen. Bayan nan a shafa Man Hulba ko Man Na'a-Na'a, ko Man habbatus sauda mai kyau. ko kuma a sanya turaren Farin Miski.
In sha Allahu za'a dace.
3. MUMTAZ : Wani magani ne wanda ZAUREN FIQHU ya hadashi musamman saboda mata wadanda sukayi haihuwa da yawa. Yana tsuke mace, kuma yana maganin kaikayi da kurarrajin gaba. Da kuma bushewa ko jin zafi yayin saduwa.
Idan an sameshi ana iya yin Matsi dashi sai bayan Awa guda ko awa biyu aje awankeshi da ruwan dumi. Za'a ci gaba dayi har tsawon sati uku.
In sha Allahu za'a samu waraka daga matsalar.
WALLAHU A'ALAM.