LOKUTAN DA ALJANU SUKA FI SHIGA JIKIN MUTANE
Shaitanun Aljanu idan suna so su shiga jikin Bil Adama, sukan jira wasu lokuta na musamman domin samun cikakkiyar damar yin hakan.
Wadannan lokutan sun hada da:
1. Lokacin da mutum yake cikin tsananin Fushi ko 'bacin rai. (Shi fushi daga Shaitan ne. shi kuma shaitan an halicceshi ne daga Wuta).
2. Lokacin da mutum yake cikin tsakiyar aikata wani abu na sa'bon Allah.
3. Lokacin da mutum yake cikin tsananin sha'awar aikata zina ko makamancinta. (Shi yasa mafiya yawan masu aikata istimna'i suna fama da shafar Aljanu).
4. Lokacin da mutum yake cikin tsananin murna akan abinda ya shafi sa'bon Allah.
5. Lokacin da mutum yake cikin sauraron wakokin soyayya, ko kallon wani abu na batsa.
6. Lokacin da Mace tayi shigar nuna tsaraici (indecent exposure) ko kuma Zane-zanen ado ajikinta. Ko kuma ta fesa turare mai Qarfi.
7. Lokacin da mutum ya manta da ambaton Allah baki daya, ya shagaltu cikin abinda Allah ba yaso.