Watarana (Azamanin Sahabbai da Tabi'ai) wani Matashin Saurayi yana tafiya zai je wani gari mai nisa sai ya wuce ta kusa da wani lambu mai 'Ya'yan itace da yawa. Har ma yaga wani Tuffah (apple) ya fado Qasa akan hanyar kusa da gonar. Kasancewar yana tsananin jin yunwa sai ya dauki wannan Tuffar yaci.
Bayan ya gama ci sai tsoro ya kamashi tunda yaci abinda ba nasa ba. Don haka ya juya ya shiga cikin garin dake jusa da wajen. yana ta cigiyar mai wannan gonar. Daga karshe aka nuna masa Dattijon dake da wannan gonar.
Yayi ma dattijon nan bayanin abinda ya faru dashi sannan ya nemi ya yafe masa Tuffar da yaci, Dattijon yace ba zai yafe ba. yace ya sayar masa, yace shi ba zai sayar ba. Daga karshe ma ya kyaleshi atsaye ya shiga gida.
Da ya fito zai tafi Masallaci da Asubah sai ya tarar da wannan matashin atsaye ya kwana yana kuka awajen da ya barshi. Sai abun ya bashi mamaki. Da ya tambayeshi mai yasa bai tafi ba? Sai yace: "Na yarda zan zauna anan garin in rika yi maka aiki har sai ka yarda ka yafe min laifin cin 'Dan itacen nan naka".
Dattijon yace "Ba zan yafe maka ba, har sai in ka yarda zaka auri yarinyata. Makauniya ce, Kurma ce, Bebiya ce, kuma gurguwa ce. Idan ka yarda zaka aureta to zan yafe maka".
Nan take saurayin nan ya amince. Bayan an daura aure sai Dattijon ya shigar dashi cikin gida domin ya ga amaryarsa. Da ya shiga dakin da take, sai yaga tunda Allah ya halicceshi bai taba ganin Mace mai kyawunta ba.. Sai ya tsaya yana mamaki.
Ita da kanta da taga Kamar ya dimauce sai tace masa "Ni nice matarka. Kuma mahaifina yace maka ni Makauniya ce tunda ban taba kallon wani abinda Allah ya haramta ba. Kuma yace maka ni kurma ce tunda kunnena bai taba sauraron wani abinda Allah ya haramta ba. Kuma yace maka ni bebiya ce tunda ban taba magana da wani wanda ba Muharramina ba. Kuma yace maka ni gurguwa ce tunda ban taba fita waje ko naje wajen da Allah ya haramta min ba".
Shi juma mahaifinta yace: "Wannan yarinyar ta haddace Alqur'ani kuma ta haddace hadisai da ilimai masu yawa. Tun tuni muke ta addu'a da fatan Allah ya kawo mata miji nagari, Sai na ganka kazo kana kuka saboda alhakin Tuffah guda daya, kana ta yawo agari har sai da ka samu gidana".
Bayan Shekara guda da daurin aure sai wannan MmAmaryar ta haifi yaro namiji kyakkyawa.. Aka sanya masa suna NU'UMAN (ABU HANEEFA).
Wannan shine tarihin auren iyayen da suka haifi IMAM ABU HANEEFAH (RAH). Daya daga cikin Tabi'ai, kuma azamaninsa ba'a samu wani Malami kamarsa ba. Ya zarce sauran Malamai wajen kaifin hadda, fahimtar ayoyi da hadisan Manzon Rahama (saww). Kuma Allah ya bashi kyawun hali da tsananin tsoron Allah da gudun duniya.
Kiyaye dokokin Allah shine babban tushen samar da Zuriyya tagari.