Assalamu alaikum da fatan dukkan Daliban ZAUREN FIQHU sun wayi gari cikin koshin lafiya. Wannan nasiha ce muke dauke da ita tare da wani labari mai ban-mamaki kuma mai tsoratarwa.
Ba labarin kowa bane illa wasu mataye guda biyu wadanda suka zarce dukkan mataye wajen Tsiyatuwa da kuma rashin rabo aduniya da lahira. Wadannan mataye sune MATAR ANNABI NOUHU DA MATAR ANNABI LUUT (as).
Alqur'ani ya bamu labarinsu cewa : "ALLAH YA BUGA MISALI GA WADANDA SUKA KAFIRTA. (MISALIN AKAN) MATAR ANNABI NOUHU DA MATAR ANNABI LUUT. SUN KASANCE KARKASHIN WASU BAYI GUDA BIYU DAGA SALIHAN BAYINMU, AMMA SAI SUKA HA'INCESU.
DON HAKA BA ZASU AMFANA MUSU KOMAI AWAJEN ALLAH BA. KUMA (ARANAR ALKIYAMAH) ZA'A CE MUSU : "KU SHIGA WUTA TARE DA MASU SHIGARTA".
(Suratut Tahreem ayah ta goma).
Akan Fassarar wannan ayar, Imam Ibnu Katheer yace : "Wajen inda Allah yake cewa "SUN HA'INCESU" ba wai ana nufin cewa su. aikata alfahsha (ZINA) bane. A'A sun ha'incesu ne acikin addini. Domin su matan Annabawa ababen kiyayewa ne daga afkawa cikin ZINA saboda alfarmar su Annabawan (as). Kamar yadda muka gabatar acikin suratun Nour.
Imam Sufyanuth Thawriy (rah) ya ruwaito daga Musa bn Abee A'ishah, shi kuma daga Sulaiman bn Qittah, yace "Naji Abdullahi 'dan Abbas yana bada labari akan abinda wannan ayar ta kunsa yana cewa:
"Ba wai zina sukayi ba. amma ha'incin Matar Annabi Nouhu, ta kasance tana gaya ma mutane cewa wai "SHI MAHAUKACI NE".
Amma ha'incin da Matar Annabi Luut tayi, ta kasance tana nuna ma Mutanenta (masu Luwadi) tana sanar dasu idan Annabi Luut din yayi baki (masu zuwa wajensa don su musulunta.. Sai su wadancan Fasikan suzo don yin Luwadi dasu).
Imam Al Aufiyyu ya ruwaito daga Abdullahi bn Abbas (ra) yana cewa: "Su matayen sun kasancd suna bayyana sirrin mazajen nasu ne. Sun kasance suna yi musu Leken asiri.
Matar Annabi Nouhu ta kasance idan wani yazo ya musulunta ahannunsa sai taje ta gaya ma Manyan azzaluman kafiran (su zo suci mutuncinsa har sai ya kafirta).
Ita kuma Matar Annabi Luut (as) ta kasance idan Annabi Luut yayi baki sai ta gaya ma mutanen garin masu aikata alfasha.
Dhahhaak ya karbo daga Ibnu Abbas yana cewa "BABU MATAR WANI ANNABI WACCE TA TABA YIN ZINA, SAI DAI HA'INCIN WADANNAN MATAYEN ACIKIN LAMARIN ADDINI NE".
Hakanan aka ruwaito daga Ikrimah da kuma Sa'eedu bn Jubayr da Dhahhaak da waninsu.
FA'IDODI
*********
Abubuwan da zamu fa'idantu dasu anan suna da yawa. Amma ga wasu 'yan kadan daga ciki:
1. Taurin kai irin na wasu matayen. (Idan matarka ta bijire maka taki bin umurninka, kar kayi mamaki tunda ga matan Manyan Manzannin Allah su ma sun aikata fiye da haka).
2. Duk kusancin nasabarka da wani mutumin kirki ba zata amfaneka ba, har sai kayi imani kuma ka aikata alkhairi. Kun ga dai Matayen Annabawa ne. Sun zauna dasu, sun kwanta dasu, sun haihu dasu, sun ci abinci tare dasu. Amma duk wannan bai yi amfani garesu ba, tunda sun kauce ma hanyar Imani kuma sun ha'incesu.
3. Wannan darasin yana Qara nuna mana GIRMAN LAMARIN MANZON ALLAH (SAWW) domin shi dukkan matayensa sun kasance muminai salihai, kuma manyan Malamai. Har ma suna taimaka masa wajen isar da aiken Allah (SWT).
4. KUBUTUWAR SAYYIDAH AISHA (RA) Daga dukkan wani zargin da Munafukai da Yahudawa suke yi.
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (3).