Mutane da yawa suna guje ma shirka a zahirinsu, to amma a batininsu suna aikata shirka ko yaushe..
Duk mutumin da yake ZAQAQA muryarsa yana karatun Alqur'ani ko afili, ko a sallah, in dai yana yi ne don nutane suji shi, wai don suce yana da ZAQIN MURYA, ko kuma don suce yana da Qarfin Qira'a, to wannan ya riga yayi Qaramar shirka azuciyarsa don haka ba zai samu komai awajen Allah ba.
Don haka sai ayi hattara da limaman zamani masu Maqala MICROPHONE awuyansu suna karatun sallah suna Rangwada, suna Alqunut suna rangwada.. . (yin rangwada acikin Alqunut BIDI'AH ne wanda zai iya sa mutum ya rasa ladan sallarsa).
- Duk mutumin da yake ciyar da dukiyarsa agaban mutane, domin su yabeshi, Don suce ai shi mai yawan kyauta ne, to shima wannan ba zai samu komai awajen Allah ba. Domin ya riga yayi Qaramar shirka tun anan duniya.
- Duk mutumin da yake yin Jihadi bisa tafarkin Allah, ko tsayawa akan wani lamarin addini, ko gudanar da wasu abubuwa bisa tafarkin Allah, in dai yayisu domin neman yabo daga wajen al'ummah, to shima ba zai samu komai awajen Allah ba. Domin ya riga ya zubda ladansa tun anan duniya yayi Qaramar shirka.
Shi yasa Manzon Allah (saww) yace: "KU KIYAYI YIN QARAMAR SHIRKA". Sai Sahabbai suka ce : "Shin menene Qaramar shirka?" Sai yace : "RIYA (Yin aikin ibadah domin neman yabo awajen Mutane).
Ya Allah ka kiyayemu daga Qaramar shirka da babbar Shirka. Ka gyara mana zukatanmu ka tsaftace mana dukkan tafiyarmu zuwa gareka.