A ranar 24 ga watan Agusta inda yan Kasar Ukraine a fadin duniya suke murnar ranar samun yancin kai, Jakdan Ukraine dake Najeriya ya bayyana cewa Kasar shi zata taimaka ma Najeriya wajen yakar Boko Haram.
Ambasadar Valerii Aleksandruk yace: “Ina alfarin kasancewa Jakada a Najeriya. Najeriya kasa ce mahimmiya mai taka rawa ba wai kawai a Yammain Afirika ba, a suka Nahiyar. Kasar Ukraine na ba hudda da Najeriya kulawa ta musamman. Yace:
“Ni a matsayina na Jakada, zanyi Iya bakin kokari na domin ganin an habbaka hudda mai kyau da Najeriya. Ina sa ran dangantakar mu zata kara karfin musamman a wannan muhimmin lokaci a Najeriya.
“Ina fatan zamu bude wani sabon shafi na danganta tsakanin Najeriya da Ukraine. Ukraine nada kyakkyawan dangantaka da Najeriya musamman wajen cinikayya da saka hannun jari.
“Zamuyi kokari mu bude wani kwamishan tsakanin Najeriya da Ukraine wanda zaya shafi tattalin arziki, da tsaro. Mista Aleksandruk ya kuma jaddada cewa kasar shi shirye take data taimaka ma Najeriya.”