Ko kun san cewa duk abubbuwan da suka kunshi ‘ya’yan itatawa na da muhimmanci a wajen gyaran jiki? Akwai ‘ya’ayan itatuwa ko kwallonsu da ke karrama kwalliyar mace ko namiji. Don haka ne a yau na kawo muku. Domin idan akwai wadanda suke son magance wani matsalar fata ko da ko na son sanya murya zaki ce za su san irin yadda zasu magance matsalolinsu.
Domin zakin murya
Za’a sami ganyen mangoro sannan sai a tafasa ruwan ana sha kullum domin samin zakin murya. Akwai matan da su ke da manyan murya da in sun yi magana sai a dauka namiji ne wannan na iya magance musu nasu matsololin. Za’a iya shan wannan ruwan sau biyu ko uku a rana.
Domin kunar fata
A sami kwallon dabino kamar kwallo 10 sai a gasa ta sannan a daka ya yi laushi. Bayan haka, sai a sami man kwakwa a hada garin kwallon dabino da shi. Sai a rinka shafawa a inda a ka kone.
Domin magance hurhurar kai
A sami ganyen kori da ganyen aloe bera da ganyen lalle. Sai a daka su guri daya. Bayan an yi hakan, sai a shafa a gashi mai hurhura. Sannan sai a jira na rabin awa kamin a wanke. Yana da kyau ana amfani da wannan hadin kamar sau 3-4 a sati.
Domin samin fata mai laushi
Sami nutmeg da madara bayan an nika nutmeg din, sannan sai a zuba madara a ciki. Sai a shafa a jiki kullum kamin a yi wanka. A bari ya bushe a fatar jiki kamin a wanke. Yin hakan kullum na sanya fata sulbi.