Assalamu alaikum Mallam ina da tambaya...
Tambayan shine.
Mutane sukanyi mua'amala da aljannu a bisa rashin sani. Wani lokacin mutun zaiga gurgu ko mabaraci yaji tausayi sai ya taimaka mishi.. Alhali be san cewa ashe aljani bane.
Sai wannan aljani yaji dadin abunda wannan bawa yayi mishi na taimako. Shine yace zai saka mishi da kyauta ta dukiya....
Shin yaya matsayin wannan dukiya agare shi?
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Idan Aljani ya baka kyauta, ya halatta ka karba. Musamman in dai dukiyarsa ce tasa ta kansa. Amma idan satowa yakeyi, ko kuma ya bukaci wani abu daga gareka, to kar ka amince masa.
Kuma anan akwai abubuwan lura guda biyu. Kuma kowannensu yana da hatsari sosai ga rayuwar mutum:
1. NA FARKO: Yana da wahala aljani ya yarda ya taimaki Dan Adam, harma ya rika bashi dukiya ba tare da komai ba. Dole sai ya sanya Dan Adam din ya rika yi masa wata hidima wacce zata kautar dashi daga kan hanyar Allah.
Misali kamar yin sadaka gareshi, ko yanka, ko kuma ya hanashi yin Sallar Juma'a, ko sallar La'asar. Ko kuma ya hanashi yin sallah da alwala, ko kuma ya sanyashi ya rika wulakantar da Alqur'ani mai girma, ko kuma ya rika zama da Janabah.
To kaga duk wanda ya aikata guda daga cikin abubuwan nan to ya kafirta kenan. Idan bai tuba ya komo Musulunci ba, to zai mutu kafiri kenan.
2. ABU NA BIYU : Akwai 'yan dampara wadanda suke hada kai da junansu suna buga ma mutane waya, suce musu wai su Aljanu ne. Tare da yi musu irin wannan bayanin da kayi mun.
zasu ce maka wai watarana suna yin bara a Masallacin Juma'ar garinku, ka basu sadaka. Don Haka yanzun kaima zasu taimaka maka. Zasu ce maka wai kayi sadakar Alqur'ani ds dabino, etc.
Daga karshe zasu yi kokari su tsafe maka zuciyarka yadda zaka rika bin umurninsu ba tare da yin shawara da kowa ba... Daga karshe zasu wawushe maka dukiyarka, su gusar maka da hankalinka, sannan su rabu dakai.
Shima irin wannan yana faruwa sosai. Yanzu haka ina da lambobin irin wadannan Aljanun Qaryar da yawa acikin contacts dina. na samu ne ta wajen Marassa lafiyan da suke zuwa wajenmu.
like us on facebook fb.com/1arewa