Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta ce 'yan kasar kusan su 12,000 sun fara isowa gida daga iyakar jamhuriyar Kamaru bayan da aka ba su umurnin su bar kasar.
NEMA ta ce mutanen sun soma isa kauyen Sahuda da ke garin Mubi a jihar Adamawa.
'Yan gudun hijira -- wadanda akasarinsu 'yan Jihar Borno ne -- wadanda suka gudu daga hare-haren da 'yan Boko Haram su ke kai wa yankunansu, na samun mafaka ne a kasar Kamaru.
Sai da jami'an shiga da fice na Najeriya da jamian tsaro suka binciki mutanen da suka dawo gida.
Hukumar NEMA ta ce kawo yanzu karbi 'yan gudun hijira 1,121 daga jami'an shiga da fice na Najeriya a iyakar, inda ta tura 650 daga cikinsu zuwa jihar Borno, yayinda ragowar har yanzu na sansanin 'yan gudun hijira da ke Yola.