'Yan sanda a jahar Kaduna sun bayyana kera makamai a matsayin daya daga cikin manyan laifuffukan dake karuwa a jahar a halin yanzu.
Rundunar 'yan sanda jahar ta kuma nunawa manema labarai wasu wadanda ake zargi da tafka miyagun laifuffuka kamar fashi da makami da sace-sacen motoci da 'yan ta'addar unguwanni wadanda aka fi sani da 'yan sara- suka.
Rundunar 'yan sandan ta ce, ta kuma damke wasu a jahar da ke kerawa 'yan fashi makamai musamman bindigogi.
Alhaji Umar Usman Shehu, kwamishinan 'yan sanda a Kaduna ya fadawa manema labarai cewa 'an samu wurare daban-daban da ake kera makamai a wasu kauyuka da suka hada da Jagundi na karamar hukumar Jema'a da kuma Kachia.
Ya ce 'mun kama mutanen kuma mun sami makamai iri iri da suka hada da AK47 da magazin da albarusai da dai sauransu'